Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana rasuwar tsohon ɗan majalisar tarayya kuma ɗaya daga cikin fitattun jagororin gwagwarmayar tabbatar da dimokraɗiyya, Chief Ralph Obioha, a matsayin babban rashi ga iyalansa da Najeriya.
Obioha, wanda ya rasu ranar 3 ga Oktoba, 2026 yana da shekara 80, ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka taka muhimmiyar rawa a ƙungiyar NADECO wajen yaƙin dawo da mulkin dimokraɗiyya bayan soke zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Yuni, 1993.
A cikin saƙon ta’aziyyarsa, Tinubu ya bayyana Obioha a matsayin ɗan ƙasa mai kishin dimokraɗiyya, wanda ya sadaukar da wani ɓangare na rayuwarsa wajen fafutukar ganin Najeriya ta koma tsarin mulkin farar hula.
- Yabon Bala Mohammed ga Tinubu ya haifar da cece-kuce kan takarar Makinde
- Sabuwar jakadar Najeriya a Italiya ta miƙa takardun amincewarta ga Mattarella
- NCAOOSCE ta fara ƙidayar Almajirai da wayar da kan masu kula da su a Kano
Shugaban ya ce marigayin ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka tsaya tsayin daka wajen kare dimokraɗiyya, adalci, bin kundin tsarin mulki da kuma ’yancin ’yan Najeriya na zaɓar shugabanninsu, duk da irin matsin lambar da masu fafutukar suka fuskanta a lokacin mulkin soja.
Tinubu ya kuma tuna da gudunmawar Obioha a matsayin ɗan majalisa, ɗan kasuwa da kuma jagoran siyasa, yana mai cewa irin sadaukarwar da ƙarniinsa ya yi a lokutan da suka fi wahala bai kamata a manta da ita ba.
Shugaban Ƙasar ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, al’ummar Abia, Ohanaeze Ndigbo, ’yan NADECO da sauran ’yan Najeriya da suka yi rashin Obioha, tare da addu’ar Allah Ya ba iyalansa haƙuri, Ya kuma jiƙan marigayin.
Obioha ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka rattaba hannu kan kafa NADECO a shekarar 1994, sannan ya taka rawa wajen ayyukan ƙungiyar daga ƙasashen Kanada da Amurka a lokacin da ake fafutukar dawo da dimokraɗiyya.
A watan Yunin 2026, Tinubu ya ba Obioha lambar yabo ta ƙasa saboda gudunmawarsa a gwagwarmayar 12 ga Yuni, sai dai marigayin ya ƙi karɓar kyautar, yana mai danganta matakin da damuwarsa kan rashin tsaro da kuma tsare Nnamdi Kanu.
Tinubu ya ce abin da ya kamata a riƙa tunawa da shi game da Obioha shi ne jajircewarsa, imaninsa da abin da ya yi imani da shi, da kuma yadda ya sadaukar da kansa wajen ganin an samu Najeriya mai ƙarfi da dimokraɗiyya.