Sabuwar jakadar Najeriya a Jamhuriyar Italiya, Abimbola Tolulope Samuel Reuben, ta miƙa takardun amincewarta ga shugaban ƙasar Italiya, Sergio Mattarella, a fadar shugaban ƙasar da ke Quirinale, Rome.

An gudanar da bikin ne a ranar 28 ga Satumba 2026, inda shugaban Italiya ya karɓi takardun amincewar sabuwar jakadar Najeriya tare da sauran sababbin jakadun ƙasashe daban-daban.

Bayan miƙa takardun, Ambasada Reuben ta gana da Shugaba Mattarella, inda ta isar masa da gaisuwar Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ga gwamnatin da al’ummar Italiya.

A yayin ganawar, jakadar ta jaddada muhimmancin dangantakar diflomasiyya da ke tsakanin Najeriya da Italiya, tare da bayyana aniyar Najeriya na ƙara bunƙasa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.

Tattaunawar ta kuma mayar da hankali kan hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannoni da suka haɗa da kasuwanci da zuba jari, makamashi, noma da samar da abinci, ƙaura da hulɗa da ’yan ƙasashen waje, ilimi, al’adu da masana’antun ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma tsaro.

Bikin ya fara ne da karramawar sojojin tsaron fadar shugaban ƙasar Italiya, Corazzieri, a fadar Quirinale, wanda ya nuna a hukumance fara aikin diflomasiyya na Ambasada Reuben a matsayin wakiliyar Najeriya a Italiya.

Shugaba Tinubu ya amince da naɗin Reuben a matsayin jakadar Najeriya a Rome a cikin jerin jakadun da ya tura zuwa ƙasashe daban-daban a watan Maris na 2026.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *