Rundunar Operation Hadin Kai ta ce dakarunta sun fatattaki wani hari mai tsanani da ’yan ta’addan ISWAP suka kai wa sansanin 101 Special Forces Battalion a Kukawa, Jihar Borno.
A cewar rundunar, ’yan ta’addan sun kai harin ne daga bangarori huɗu, amma sojojin suka mayar da martani tare da taimakon rundunar sama, lamarin da ya tilasta wa waɗanda suka tsira tserewa.
- Hukumar tace Fina-Finai ta amince da rashin lafiyar Tijjani Gandu
- INEC ta tabbatar da zama tsaka-tsaki a Zaɓen 2027
Rundunar ta ce binciken farko ya nuna cewa an hallaka sama da ’yan ta’adda 25, yayin da aka gano gawarwaki 14. An kuma kwato makamai da alburusai, ciki har da bindigogin AK-47 guda shida.
Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa wasu sojoji sun rasa rayukansu yayin artabun, tana mai jajanta wa iyalansu tare da yabawa jarumtakarsu da sadaukarwarsu wajen kare ƙasa.
Rundunar ta ce dakarunta na ci gaba da binciken yankin domin gano karin makamai, bibiyar ’yan ta’addan da suka tsere da kuma hana su sake tattara ƙarfi.