Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano ta amince da rahoton rashin lafiyar mawaki Tijjani Gandu, wanda ya gabatar da shi a matsayin dalilin da ya sa bai samu damar amsa gayyatar da hukumar ta yi masa ba.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, 6 ga Oktoba, 2026, kan batun rashin lafiyar mawakin, bayan gayyatar da aka yi masa dangane da wata waka da ya saki wadda ake zargin ta saba wa dokar da ta kafa hukumar.

Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, ANIPR, ya fitar a ranar Talata.

A cewar sanarwar, lauyan mawakin ne ya gabatar wa da hukumar da rahoton da ke ɗauke da bayanan rashin lafiyar Tijjani Gandu, inda ya bayyana rashin lafiyar a matsayin dalilin da ya hana mawakin halartar gayyatar a lokacin da aka tsara.

Hukumar ta ce bayan jami’an lafiya sun tabbatar da sahihancin rahoton, ta gamsu da bayanan da aka gabatar, tare da amincewa da rashin lafiyar a matsayin ingantaccen dalilin da ya sa mawakin bai samu damar amsa gayyatar ba.

Sai dai hukumar ta bayyana cewa za ta ci gaba da sa ido kan lamarin har zuwa lokacin da mawakin zai samu sauƙi, domin tabbatar da bin dokar da ta kafa Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano.

Hukumar ta kuma yi wa Tijjani Gandu fatan samun sauƙi, tare da addu’ar Allah Ya ba shi cikakkiyar lafiya mai ɗorewa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *