Kamfanin NNPC Ltd. ya bi sahun masu ruwa da tsaki a masana’antar mai da iskar gas wajen taya Hukumar Kula da Harkokin Mai ta Sama ta Najeriya (NUPRC) murnar cika shekaru biyar da kafuwa.
Babban Daraktan Gudanarwa na NNPC Ltd., Injiniya Bashir Bayo Ojulari, wanda ya jagoranci tawagar kamfanin a wajen bikin da aka gudanar a Abuja, ya taya hukumar murnar wannan matsayi, tare da jaddada muhimmancin haɗin gwiwa wajen ƙarfafa ɓangaren hako mai na Najeriya.
- INEC ta tabbatar da zama tsaka-tsaki a Zaɓen 2027
- Hukumar tace Fina-Finai ta amince da rashin lafiyar Tijjani Gandu
Ojulari ya kuma sake tabbatar da aniyar NNPC Ltd. na ci gaba da aiki tare da NUPRC wajen bunƙasa arzikin man fetur, ƙara yawan hako mai, haɓaka samar da iskar gas da kuma samar da ƙarin daraja ga Najeriya da ’yan ƙasar.