Majalisar ƙungiyar kwadago ta Najeriya, NLC, reshen Abuja, ta umarci ma’aikatan babban birnin tarayya da su fara yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Laraba, sakamakon rashin warware wasu rikice-rikicen aiki da suka shafi malaman makarantun FCT.

Matakin ya biyo bayan ƙarewar wa’adin kwanaki bakwai da ƙungiyar ta bai wa gwamnatin FCT, ƙarƙashin jagorancin Ministan Abuja, Nyesom Wike, domin magance matsalolin da suka shafi ƙarin girma da ci gaban malaman makarantu.

Shugaban NLC na FCT, Knabayi Adalo, ya ce ɗaya daga cikin manyan buƙatun ƙungiyar shi ne cire sharadin samun gurbin aiki kafin malami ya samu ƙarin girma, wanda ya ce yana haifar da tsaikon aiki da rage ƙwarin gwiwar malamai.

Ƙungiyar ta kuma nemi a janye wasiƙun mayar da wasu manyan daraktoci aiki ko rage musu matsayi, musamman waɗanda suka ci moriyar dokar shekarar 2022 da ta tanadi shekarun ritayar malamai, tare da ba malaman da suka cancanci jarabawar ƙarin girma ta 2025 damar rubuta jarabawar tare da rukunin 2026.

NLC ta kuma buƙaci a sake duba tsarin gudanar da Hukumar Ilimin Sakandaren FCT da Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta FCT, tana mai cewa matakan da gwamnatin FCT ta ɗauka kawo yanzu ba su samar da mafita mai gamsarwa ba.

A nasa ɓangaren, gwamnatin FCT ta bayyana cewa manufofin da suka shafi ƙarin girma da sauya wurin aiki suna da alaƙa da ƙa’idojin aikin gwamnati, da guraben da aka amince da su da kuma tsarin gudanar da ma’aikata.

NLC ta umarci ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu a FCT, da ƙungiyoyin da ke ƙarƙashinta, da su janye ayyukansu har sai an warware buƙatunta.

Ta kuma kafa kwamitocin sa ido domin tabbatar da bin umarnin yajin aikin a sassa daban-daban na babban birnin tarayya.

Yajin aikin na iya shafar makarantu, asibitoci, ofisoshin gwamnati da sauran ayyuka a Abuja, yayin da ake jiran ƙarin tattaunawa tsakanin NLC da gwamnatin FCT domin samo hanyar da za ta kawo ƙarshen rikicin.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *