Wani lamari mai ban mamaki ya auku a filin jirgin saman Frankfurt na kasar Jamus, inda cutar zazabbin cizon sauro wato Maleriya ta yi sanadiyyar mutuwar ma’aikatan filin jirgin su biyu, bayan cizon wani sauro da ake zargin ya shiga cikin jirgin saman daya taso daga kasashen da ke da annobar.

Rahotonni daga Jamus na cigaba da fadada game da adadin ma’aikatan da suka kamu da zazzabin, wanda adadin su kawo yanzu aka hakkake sun kai Shida, kuma kafin gano lalurar da wuri Biyu daga cikin su ka riga mu gidan gaskiya.

Wani rahoton Hukumar binciken cututtuka ta Jamus (Robert Koch Institute) ya bayyana cewa a Jamus ko Turai, likitoci ba sa tsammanin samun zazzabin cizon sauro ga mutumin da bai yi balaguro zuwa kasashen Afirka ko Asiya ba, wannan ce ta sanya jinkirta gano cutar cikin gaggawa har ta tsananta.

Hukumomin lafiya sun bayyana cewa wani sauro ne mai dauke da cutar ne ya makale a cikin jirgin sama zuwa Turai, sai dai kawo yanzu, Hukumomin filin jirgin saman Frankfurt sun tashi tsaye wajen kafa tarkon kame sauro a ko’ina a filin, domin mika su ga cibiyar nazarin cututtuka masu alaka da kasashe masu zafi da ke Belgium, domin gudanar da binciken gano takamaiman kasar da sauron ya fito.

Wannan lamari ya tayar da hankalin masana kiwon lafiya a Jamus, ganin cewa zazzabin cizon sauro abu ne mai matukar karanci a kasar idan har mutum bai yi tafiya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *