Babban Dogari (ADC) da kuma Babban Jami’in Tsaron Lafiya (CSO) na Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, suna tsare a Hedikwatar ’Yan Sandan Najeriya da ke Abuja.Exploring Ba Vi’s Dragon Fruit Garden [NếmTV]null
Hukumar ’Yan Sanan Najeriya tana tsare ADC da CSO na gwamnan ne tun ranar Alhamis 20 ga watan nan na Agusta, 2026 ne, a yayin da majiyoyi da dama ke cewa tsarewar na da alaka da rikicin siyasar cikin gida da ke kara tsanani a Jam’iyyar APC mai mulkin jihar.
Ko da yake rundunar ’yan sanda ba ta bayyana dalilin tsare jami’an biyu ba, wasu majiyoyi na zargin an dauki matakin ne bayan umarnin Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Tunji Disu, a sakamakon koke-koke da suka shafi wasu manyan masu ruwa da tsaki a APC.
Aminiya ba ta iya tabbatar da kanta ba kan zargin cewa daga ina ne umarnin tsare jami’an ya fito.
- ’Yan sanda sun tarwatsa maboyar ’yan bindiga a Kaduna
- Sama da ‘yan ta’adda 150 suka miƙa wuya a mako
Ci gaba da tsare jami’an da ke da alhakin kare lafiyar wani gwamna mai ci ya janyo fargaba a tsakanin masu ruwa da tsaki kan harkokin siyasa da tsaro, musamman saboda muhimmiyar rawar da suke takawa wajen kare gwamnan.
Sun kuma yi gargadin cewa shigar da hukumomin tsaro cikin rikice-rikicen cikin gida na jam’iyya na iya rage amincewar jama’a da hukumomin tabbatar da doka, tare da kara dagula yanayin siyasa gabanin zaɓen 2027.
Wasu majiyoyi na zargin lamarin yana da alaka da rikicin neman iko a Jam’iyyar APC ta Jihar Katsina, wanda ke kara daukar sabon salo.
Majiyoyin jam’iyyar da dama sun bayyana rikicin a matsayin ja-in-ja tsakanin manyan bangaren da ke goyon bayan Gwamna Radda, da kuma bangaren da ke biyayya ga Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Mai Bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu Shawara ta Musamman kan Harkokin Siyasa.
A cewar majiyoyin, rashin jituwar bangarorin biyu ta ƙara tsananta a cikin ’yan watannin nan, musamman kan wanda zai mallaki tsarin siyasar jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.
Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa rahoton tsare jami’an tsaron Gwamna Radda na daga cikin manyan abubuwan da suka fi nuna yadda rikicin cikin gida na APC a Katsina ya ƙara tsananta.
Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa an kama jami’an ne kan zargin lalata allunan tallar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Mataimakinsa, Kashim Shettima, da kuma Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari.
Kafar yada labarai ta aridar Katsina Times ta ruwaito, ana zargin jami’an tsaron gwamnan da masaniyar abin da ya faru, da kuma yiwuwar hannunsu a ciki.
Lamarin na lalata allunan tallan ya biyo bayan wani jawabi da Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa, ya yi a wani taro da aka gudanar a wani otal da ke Maƙera, wanda daga baya ya koma ofishinsa.
A cikin jawabin, an ruwaito Masari yana cewa: “Gwamnatin Tarayya ta bayar kuma tana bayar da duk abin da ya kamata, amma mu ne ke ba ku.”
Rahotanni sun ce wasu magoya bayan Gwamna Radda na kallon wannan jawabi a matsayin zargin Kabir Masari na adawa da Gwamna Radda.
A halin da ake ciki, rahotanni sun ce Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir, da shi kansa Gwamna Radda, sun yi ƙoƙarin ganin an saki jami’an tsaron biyu domin su ci gaba da aikinsu.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ƙoƙarin nasu bai yi nasara ba, domin har yanzu jami’an biyu suna tsare a hannun ’yan sanda a Abuja.