An gudanar da taron Maulidi a Old Parade Ground da ke Babban Birnin Tarraya a Abuja
Inda aka samu halartar manyan baƙi da dama, daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa, Comrade Nasiru Kabir, da Hakimin Kyado Kuci, Alhaji Suleman Dodo.
A jawabinsa, Comrade Nasiru Kabir ya ja hankalin al’umma kan muhimmancin wannan wata mai albarka, tare da kira ga jama’a da su yi amfani da wannan lokaci wajen ƙara kusantar Allah ma ɗaukakin sarki da kuma tunawa da koyarwar da Annabi Muhammad (SAW) yayi.
Shi ma Hakimin Kyado Kuci, Alhaji Suleman Dodo, ya buƙaci al’ummar Musulmai da su zauna lafiya, su ƙarfafa zumunci da haɗin kai, tare da yin koyi da kyawawan ɗabi’un Annabi Muhammad (SAW).
Haka kuma, taron ya samu halartar al’umma da sauran manyan baƙi da suka zo daga garuruwa daban-daban domin gudanar da Maulidin tare da jaddada muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’umma.
An gudanar da addu’o’i da wa’azuzzuka, inda malamai suka tunatar da mahalarta taron muhimmancin koyi da kyawawan ɗabi’un Annabi Muhammad (SAW), da kuma ƙarfafa zumunci da taimakon juna, musamman wajen nuna tausayi, haƙuri da girmama juna a tsakanin al’umma.