Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar OO Oluyede, ya bayyana cewa ƙulla ƙarin alaƙa da Masarautar Saudiyya a fannin tsaro zai taimaka wajen inganta sha’anin tsaro a Najeriya tare da ƙara ƙarfafa ƙwarewar rundunonin tsaron ƙasar.
Janar Oluyede ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar bakuncin Jakadan Masarautar Saudiyya a Najeriya, Yousef bin Mohammed Al-Balawi, wanda ya kai ziyara Hedikwatar Tsaron Najeriya domin tattauna hanyoyin zurfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.
- Rayuwar ’yan Najeriya na kara tsananta – Farfesa Bongo
- Shugaban ƙasa ya bayar da umarnin ceto mutanen da aka sace a Jihar Neja
- Tinubu – Hausa ƙabilace dake taka muhimmiyar rawa wajen haɗin kan Najeriya
Babban Hafsan Tsaron ya jaddada muhimmancin dangantakar Najeriya da Saudiyya, yana mai cewa ya kamata a ci gaba da faɗaɗa hanyoyin haɗin gwiwa musamman a fannonin da za su ƙara inganta ƙarfin aiki da kwarewar Rundunonin Sojin Najeriya.
A nasa jawabin, Jakadan Saudiyya a Najeriya, Yousef bin Mohammed Al-Balawi, ya bayyana Najeriya a matsayin muhimmiyar ƙawa ga ƙasarsa a nahiyar Afirka, inda ya sake jaddada aniyar Saudiyya ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da Najeriya musamman a ɓangaren tsaro da soja.
Ya ce ƙarfafa hulɗar hukumomi da ƙwarewa tsakanin rundunonin tsaron ƙasashen biyu zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro da suka shafi ƙasashen.