Najeriya ta samu gagarumin ci gaba wajen daidaituwar tattalin arziki, tun bayan cire tallafin man fetur da kuma sassauta tsarin musayar kudaden waje, amma hakan ya zo ne da tsadar tabarbarewar rayuwar ’yan kasa, karuwar talauci da kuma rashin daidaito tsakanin masu karfi da marasa karfi.
Farfesa Bongo Adi, masanin tattalin arziki ne, kuma ya bayyana cewa ya gano hakan yayin da yake nazarin manufofin tattalin arzikin Gwamnatin Tarayya cikin shekaru uku da suka gabata, musamman tasirin cire tallafin man fetur.
Adi ya ce ko da yake matakan da gwamnati ta dauka sun taimaka wajen rage wasu matsalolin da suka dade suna damun tattalin arzikin kasar, ciki har da matsin lamba kan kudaden gwamnati da kasuwar musayar kudaden waje, tasirin wadannan sauye-sauye ya fi bayyana wajen rayuwar talakawa.
Ya ce cire tallafin man fetur ya sauya tsarin tattalin arzikin Najeriya, inda farashin man fetur ya tashi tare da kara kudin sufuri da na kayayyaki da ayyuka.
- Tinubu – Hausa ƙabilace dake taka muhimmiyar rawa wajen haɗin kan Najeriya
-
Bai kamata Najeriya ta zama filin kisan gilla ba – Obi ga Gwamnatin Tarayya
-
Babangida muhimmin turke ne dake tallafe da Najeriya- Muhammad Idris
Wannan, a cewarsa, ya kara matsin lamba kan masu karamin karfi da ke fama da hauhawar farashin abinci da sauran bukatun yau da kullum.
Masanin ya bayyana cewa sassautawa da cire ka’idojin a kasuwar kudaden waje ma ya taimaka wajen samar da wani tsarin da ya fi samar da yanci akan takardar Naira, sai dai faduwar darajar kudin ta kara tsadar kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje.
A cewarsa, duk da cewa wasu alamomin tattalin arziki na iya nuna cewa Najeriya na samun kwanciyar hankali, hakan baya nufin a auna nasarar manufofin tattalin arziki da wadannan alkaluma kadai ba.
Ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda sauye-sauyen ke shafar rayuwar talakawa, samar da ayyukan yi, damar sayen kayan amfani da kuma yadda masu karamin karfi ke iya biyan bukatunsu na yau da kullum.
Adi, ya kuma yi gargadin cewa idan ba a dauki karin matakan rage radadin tattalin arzikin da jama’a ke fuskanta ba, gibin da ke tsakanin masu hannu da shuni da sauran al’umma na iya kara fadada.
Ya bukaci gwamnati da ta hada manufofin daidaita tattalin arziki da matakan da za su taimaka wa ’yan kasa kai tsaye, musamman ta hanyar samar da ayyukan yi, tallafawa masu kananan sana’o’i da inganta ababen more rayuwa.
A cewarsa, samun daidaiton tattalin arziki yana da muhimmanci, amma dole ne a tabbatar da cewa amfanin sa ya isa ga mafi yawan ’yan Najeriya, ba wai ya tsaya kan alkaluman tattalin arziki kawai ba.