Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi Allah-wadai da hare-haren kisa da garkuwa da mutane da aka samu a wasu sassan yankin Arewa ta Tsakiya, yana mai gargadin cewa bai kamata Najeriya ta zama “filin kisan gilla” ba.

Obi ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, bayan hare-haren baya-bayan nan da suka faru a jihohin Binuwai da, Pilato da Naija

Ya bayyana hare-haren a matsayin gaggawar tsaron ƙasa, tare da kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su ɗauki matakan gaggawa da tsauri domin kare al’ummomin da ke cikin haɗari da kuma hana ƙarin zubar da jini.

Ya ce: “Me ke faruwa da ƙasarmu? A cikin kwanakin baya-bayan nan, mun fuskanci munanan hare-hare a jihohin Benue, Plateau da Niger, waɗanda suke makwabtaka da juna a yankin Arewa ta Tsakiya.”

Obi ya ce a Mangu, Jihar Pilato, an ruwaito cewa aƙalla mutane 23 ne aka kashe a harin Jwak Maitumbi, yayin da mazauna yankin suka ce adadin waɗanda aka kashe ya haura 30. An kuma bayar da rahoton lalata gidaje sama da 45.

A Borgu, Jihar Naija, ya ce hare-haren baya-bayan nan sun kashe sama da mutane 40, sannan aka yi garkuwa da sama da 100, duk da cewa ana takaddama kan waɗannan alkaluma.

Ya ce wannan na faruwa ne a daidai lokacin da tashin hankali ke ci gaba da addabar Jihar Binuwai, inda al’umma ke fuskantar maimaita kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma lalata gidaje da hanyoyin neman abinci da rayuwa.

Obi ya ce ana kai wa ‘yan Najeriya hari a cikin garuruwansu duk da cewa ƙasar ba ta cikin yaƙi a hukumance.

Tsohon Gwamnan Jihar Anambra ya bukaci gwamnatoci a dukkan matakai da su ƙarfafa matakan tsaro, inganta tattara bayanan sirri da kuma saurin kai ɗauki, tare da ceto ‘yan Najeriya da aka yi garkuwa da su da kuma kama tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a hare-haren.

A cewarsa kamata ya yi gwamnati ta fi mayar da hankali kan hana hare-hare kafin su faru, maimakon jira sai an rasa rayuka sannan a mayar da martani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *