Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Janar Tukur Yusufu Buratai (mai ritaya), ya bukaci ‘yan Nijeriya da su hada kai domin kare ikon kasa da mutuncinta, a daidai lokacin da ake gudanar da shari’a a Amurka game da yiwuwar sakin wasu takardu da suka shafi Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Buratai ya yi wannan kiran ne a cikin wata takarda da ya fitar mai taken, “Nijeriya Farko: Hujjojin Kare Ikon Kasa da Mutuncinta — Ta Hangar Kishin Kasa da Rashin Bangaranci.”
Ya bayyana cewa kada a kalli lamarin a matsayin matsalar shari’a ta kashin kansa da ta shafi Shugaban kasa kawai, a’a, kamata ya yi a kalle ta a matsayin abin da zai iya shafar kimar Nijeriya a idon duniya da kuma moriyar kasa.
A cewarsa, rahotanni game da takardun da ake zargin suna da alaka da binciken da aka gudanar sama da shekaru talatin da suka gabata za su iya haifar da sakamako mai fadi da ya wuce mutum guda, musamman idan suka haifar da mummunan labari game da Nijeriya a fagen duniya.
- Lafiyar mata ita ce ginshikin ci gaban tattalin arzikin Najeriya Amaechi
- Yari Ya Karɓi Naɗin Muƙamin Shugaban Kamfen ɗin Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC
- Mutane biyar sun rasu a taho-mu-gamar motoci a bababr hanyar Badagry
Buratai ya ce Kotun Gundumar Amurka ta yankin Columbia ta sanya ranar 28 ga Agusta, 2026, domin Shugaba Tinubu, Hukumar Bincike ta Tarayya (FBI) da Ma’aikatar Shari’a ta Amurka su mayar da martani kan batutuwan da suka shafi yiwuwar sakin takardun.
Ya ce alamun da FBI ta bayyar na cewa tana da bayanai “masu matukar muhimmanci” da kuma bukatarta na a yi nazarin sirri a gaban alkali ya sa lamarin ya zama mai girma, sai dai ya jaddada cewa ya kamata Nijeriya ta kalli lamarin ta fuskar moriyar kasa.
“Ba Tinubu muke karewa ba; kanmu muke karewa. Muna kare miliyoyin ‘yan Nijeriya masu kwazo ne wadanda ba a taba zarginsu da wani laifi ba, amma za su fuskanci tabon wannan tonon silili,” in ji shi.
Tsohon shugaban sojin ya bayyana cewa kasashen waje za su iya danganta zargin da ake yi wa shugaban Nijeriya mai ci da kasar kanta, hakan kuma zai shafi yadda ake kallon ‘yan Nijeriya, ‘yan kasuwa, da hukumomin kasar a ketare.
Ya nuna damuwa musamman kan yadda sakin takardun zai iya haifar da labaran gaske da na kafofin sada zumunta wadanda za su iya boye nasarorin da Nijeriya ta samu a fannin kasuwanci, fasaha, ilimi, wasanni, da masana’antun kirkire-kirkire.
Haka kuma Buratai ya nuna shakku kan muhimmancin da ya kamata a ba wa zarge-zargen da suka shafi abubuwan da aka ce sun faru kimanin shekaru 33 da suka gabata, inda ya ce daidai da mutane da al’ummomi za su iya canzawa sosai a cikin irin wannan lokaci.
A kan ikon kasa, Buratai ya ce ya kamata ‘yan Nijeriya su damu da abin da ya bayyana a matsayin faffadan tasirin shari’ar kasashen waje da ta shafi abubuwan da suka gabata na shugaban Nijeriya mai ci.
Ya bayyana cewa ya kamata a magance tambayoyin da suka shafi halaye da dabi’un shugabannin siyasar Nijeriya ta hanyar tsarin mulki da hukumomin Nijeriya.
“Ba mu zabi kotun Amurka don ta tantance shugabanninmu ba. Ba mu nemi FBI ta tantance halayen shugabanmu ba.
Muna da namu tsarin, namu hukumomin, da namu dabi’un,” in ji shi.
Sai dai Buratai ya jaddada cewa kada a fassara matsayinsa da cewa yana kiran a cire shugabanni daga yin accountability (bincike ko bayani). Maimakon haka, ya ce ya kamata a bi tsarin binciken ta hanyar doka da hukumomin da suka dace yayin da ake girmama mutuncin kasar Nijeriya.
Tsohon shugaban sojin ya kuma yi gargadin yiwuwar fuskantar matsalolin tattalin arziki idan takaddamar ta haifar da mummunar illa ga kimar Nijeriya a duniya.
Ya lissafa abubuwan da za su iya shafa kamar zuba jarin kasashen waje, huldar kasuwanci ta kasa da kasa, huldar ‘yan kasashen waje (diaspora), yawon bude ido, da kuma martabar kamfanonin Nijeriya dake gudanar da ayyuka a ketare.