Mutane biyar sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya haɗa wata mota da babbar mota a babban titin Badagry da ke Legas.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa hatsarin ya faru da sanyin safiyar Asabar a yankin Sawmill, kusa da tashar motar Mowo.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA) ta ce ta samu kiran neman agaji da ƙarfe 5:16 na safe, inda nan take ta tura tawagar Dolphin Team daga sansanin Igando zuwa wurin da hatsarin ya faru.
- Gwamnatin jihar Katsina ta ƙaddamar da rahoton binciken gidaje domin inganta tsara manufofi
- Tinubu zai jagoranci majalisar yaƙin neman zaɓensa
- Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta tabbatar da sace wasu masu ibada a Ƙaramar Hukumar Borgu
Da jami’an suka isa wurin, sun gano cewa wata Toyota Camry mai lambar rajista FKJ 630KS ta yi karo kai-tsaye da wata babbar motar Iveco mai lambar rajista T28081 LA.
A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren LASEMA, Olufemi Oke-Osanyintolu, ya fitar ranar Asabar, ya ce binciken farko ya nuna cewa gudun wuce sa’a da tukin ganganci daga direban Camry ne suka haddasa hatsarin.
Sanarwar ta ce jami’an da suka shiga aikin ceto a wurin sun haɗa da LASEMA Dolphin Team da Hukumar Kashe Gobara da Ceto ta Jihar Legas da Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Legas (LASTMA) da Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Tarayya (FRSC) da kuma jami’an ’yan sanda daga sashen Morogbo.