Hukumar shirya Gasar Ƙwallon Ƙaka ta Amurka, wato MLS, ta sanar a ranar Jumma’a, 21 ga Agustan 2026 cewa ta ci tarar Lionel Messi saboda ya daki abokin karawar sa.
MLS ta ce ta ci tarar tauraron ɗan wasan ƙasar Argentina amma ba ta bayyana adadin kuɗaɗen ba.
A cewar MLS, dalilin cin tarar Messi shi ne ya aikata laifin dukan Quinn Sullivan, ɗan wasan ƙungiyar Philadelphia Union a wuya, yayin wasa da Inter Miami inda suka tashi 2-2 a ranar Laraba, 19 ga Agusta.
-
Arsenal ta lallasa Coventry a wasan bude kakar Firimiyar Ingila na bana
-
Cristiano Ronaldo ya fara kakar wasan bana da ƙafar dama
-
Galatasaray ta yi fatali da tayin Al-Hilal na yuro miliyan 150 akan Osimhen
Daga cikin dokokin MLS, akwai sashin doka da ya haramta wa wani ɗan wasa “sanya hannu a fuska, ko a kai, ko kuma a wuyan abokin karawa.”
Abokin wasan Messi, Ian Fray, shi ma an ci tarar sa saboda keta doka iri ɗaya da Messi a ƙarshen lokacin tashi daga karawar.
A wata sanarwa ta daban a ranar Juma’a, MLS ta ce ta soke jan katin da aka bai wa Cavan Sullivan, dan wasan Philadelphia Union mai shekara 16, kanin Quinn, bisa fadan da ya shiga don kare yayan sa.
Messi ya zura ƙwallo a wasan da suka tashi 2-2, wacce ta zamo ƙwallon sa ta farko tun bayan rasuwar mahaifinsa, Jorge.
Gwarzon ɗan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau 8 bai buga wasan Inter Miami na ranar 8 ga Agusta ba, ranar da mahaifinsa ya rasu.
