Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta ce an sace adadin masu ibadar Juma’a da ba a bayyana ba daga ƙauyukan Gidan Zana da Masaka da Sabon Gida da wasu ƙauyukan da ke makwabtaka da su a Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa sace-sacen jama’ar ya faru ne bayan kammala sallar Juma’a a Babban Masallacin da ke yankin Dekara.

Daga cikin mutanen da ake zargin ’yan bindiga sun sace har da mahaifin Hakimin Gundumar Dekara mai shekaru 90.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa, duk da cewa ba a rasa rai ba, an tura jami’an tsaro domin gudanar da aikin ceto.

Sai dai ya ce mummunan yanayin hanyoyi ya jinkirta kai da komawar jami’an tsaro.

Ya ƙara da cewa rushewar wata gada da ke haɗa al’ummar da hedikwatar ƙaramar hukumar ta ƙara kawo cikas ga aikin ceto cikin gaggawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *