Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta kama Prince George Buchi Nwabueze, bisa zargin sa da hannu a kafa wata hukumar bogi mai suna “National Brands Development and Made in Nigeria Special Project Office”, wadda aka gano a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa ta gano hukumar da ake zargin ta bogi ce a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume.
Shugaban ICPC, Dakta Musa Adamu Aliyu, SAN, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai na fadar shugaban kasa karin bayani bayan ganawarsa da Shugaba Tinubu a ranar Juma’a.
-
EFCC ta janye tuhumar ta take yi wa Maryam Shehu da Abubakar Abdulhamad
-
Mauludin Annabi: Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Talata a matsayin ranar hutu
Dakta Adamu ya ce an gano sabuwar hukumar bogin ne a yayin binciken da ake ci gaba da gudanarwa kan wata hukumar bogi mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council, wadda Adeyemi Matthew ke gudanarwa.
Ya ce an ware wa hukumar wani ofishi ba bisa ka’ida ba a cikin harabar ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.
Shugaban ya kuma bayar da umarnin dakatar da sakatarorin dindindin uku nan take, wadanda suka hada da M.S. Danjuma, da Injiniya Nadungu Gagare da Richard P. Pheelangwah, bisa lamarin.