Shugaban Hukumar EFCC, Mista Ola Olukoyede, ya ba da umarnin janye tuhumar da ake yi wa Maryam Isah Shehu da Abubakar Shuraim Abdulhamad a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Kotun Koli ta Tarayya da ke Abuja.
A ranar Alhamis, 20 ga Agusta, 2026, hukumar ta gurfanar da Maryam Isah Shehu a kan laifin yunkurin ɓata sunan hukumar a yanar gizo, ta hanyar wani rubutu a Shafin ta na Instagram.
Wanda ake kara na biyu Abubakar Shuraim Abdulhamad, an gurfanar da shi ne a kan tuhuma guda ɗaya na laifin ƙirƙirar bayanan-ƙarya akan hukumar ta EFCC.
Sai dai kuma, duk da cewa hukumar ta ɗauki laifukan a matsayin wanda ya sabawa Sashe na 24(2) (c) na dokar laifukan ta intanet na shekarar 2015, Shugaban EFCC ya yi la’akari da roƙon da mahaifin Maryam da sauran ‘yan Najeriya suka yi na neman sassauci, inda ya ba da umarnin janye ƙarar gaba ɗaya tare da faɗakar da jama’a kan kare kimar hukumar.
-
Ana amfani da almajirai a Abuja don yi wa masu ababen hawa sata – ‘Yan sanda
-
Mauludin Annabi: Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Talata a matsayin ranar hutu
Wannan al’amari ya sa mutane da dama na tambayar dalilin da ya sa EFCC ta ɗauki kwanaki 35 tana rike da Maryam ba tare da beli ba, kafin shigar da tuhuma ɗaya tak akan ta.
Tun da farko Maryam na zargi ne kan cin hanci da rashawa da ya shafi wani Daraktan EFCC, sai dai har yanzu hukumar ba ta bayyana wa ‘yan Najeriya ko ta gudanar da bincike mai kan zargin ba, ballantana daukar mataki.
Masu lura da al’amurra na ganin cewa garkame ɗan ƙasa na tsawon kwanaki 35 da ba shi takardar tuhuma a jajiberen ranar gurfanar da shi gaban kuliya, tamkar hana lauyoyin sa damar da tarin Mulki ya basu wajen shirya hujjoji ko kuma neman belin sa a gaggauce.
Kungiyoyin fararen hula da sauran al’ummar Najeriya na cigaba da tattaunawa game da wannan al’amari, tare da neman ba’asin ko hukumar na da hurumin kamawa, tsarewa ko gurfanar da wanda ta ke zargi da furta kalamai da basu yi mata dadi ba?