Shelkwatar rundunar ’yan sanda na Birnin Tarayya, ta ce gungun masu aikata laifuka na amfani da ƙananan yara almajirai don ruɗar direbobi a wuraren cunkoso don yi wa direbobi sata a Abuja.
Shelkwatar ’yan sandan wadda ta nuna damuwa kan lamarin, ta yi zargin cewa ɓatagarin suna baiwa yaran kuɗi Naira 500 zuwa 1,000, domin ɗauke hankalin masu ababen hawa yayin da suke kokarin sace musu kayayyaki masu daraja daga cikin motoci.
Kwamishinan ’yan sanda na Abuja, CP A M Sanusi, shi ne ya bayyana hakan yayin ganawa da mazauna yankin, inda ya ce yaran suna zuwa kusa da motoci a wuraren cunkoso su nuna kamar suna bara ko neman taimako, sannan su kuma masu aikata laifin su yi amfani da damar wajen sace wa masu ababen hawa kayayyakin su.
-
Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS ta cafke wani sojan gona a Abuja
-
Mambobin ISWAP huɗu sun miƙa wuya
-
Rundunar ’yan sandan Sokoto ta gurfanar da wadanda ake zargi da satar babura a gaban kotu
“Manyan ne ke ɗaukar wadannan yara aiki, idan suka tsayar da mota ko su zo kusa da kai kamar suna bara ko neman wani abu, su ruɗe ka, lokacin da ka ba su hankalin ka, sai sauran su saci kayan ka daga gefen motar,” in ji shi.
Kwamishinan ya ce ’yan sanda sun gano a wasu lokuta inda masu fashin sukan ji wa mutane rauni, ciki har da wata mata da suka ji mata rauni a kunne, lokacin da suka yi yunƙurin wafce mata ’yan kunne.
Kwamishinan ya ƙara da cewa saboda ƙarancin shekarun yaran, ba za a iya gurfanar da yawancin su ba, a saboda haka Shelkwatar na aiki tare da hukumomin kula da walwalar jama’a domin sake gyara halayyan yaran da kuma mayar da su ga iyayensu.
Kwacen waya da sauran kayan amfani na karuwa musamman a yan kwanakin nan a kwaryar babban birnin, sakamakon yawaitar mabarata da cunkoson ababen hawa, lamarin dake sanya hukumomin tsaro tsayawa a irin wadannan wurare.
