Wasu mambobin ƙungiyar ISWAP huɗu sun miƙa wuya ga dakarun sojin Najeriya, bayan tsananta matsin lambar da sojoji ke yi wa ƙungiyar a yankin Marte ta Jihar Borno.
Rahotanni sun ce mutanen huɗun an sace su ne a wurare daban-daban a Borno tare da tilasta musu shiga ƙungiyar ISWAP, an bayyana sunayensu da Isha Bukar mai shekara 19, Abubakar Alkali mai shekara 25, Tijani Mele mai shekara 15 da Abubakar Mohammed Mairiga mai shekara 24.
Bukar ya ce babban ɗan uwansa, wanda ke cikin kungiyar ISWAP, ne ya sace shi kimanin shekara guda da ta wuce tare da kai shi sansanin Arinna Chiki da ke Marte.
Shi kuwa Alkali ya ce mayaƙan ISWAP sun sace shi ne yayin da yake aikin gona a ƙauyen Buluwa. Mele ya ce ɗan uwansa ne ya sace shi yayin da yake neman itacen girki a yankin Gudunbali, yayin da Mairiga ya ce an sace shi ne lokacin da yake kamun kifi a Dowoshi, cikin ƙaramar hukumar Kukawa.
Sojoji sun ce ci gaba da kai hare-haren sama da kuma wasu dabarun yaƙin tunani sun ƙara tabarbare yanayin rayuwa a sansanin.
Hakan ya sa mutanen huɗun suka yanke shawarar tserewa daga sansanin kafin daga bisani su miƙa wuya ga dakarun sojin Najeriya.
Bayan miƙa wuya, an kai su hedikwatar Sector 3 domin ci gaba da bincike da tantance bayanansu. Sun kuma bayyana cewa sansanin Arinna Chiki na daga cikin manyan mafakar ISWAP, kuma wasu shugabannin ƙungiyar da suka hada da Abu Salim da Abu Riana ne ke jagorantar sansanin.
- Rundunar ’yan sandan Sokoto ta kashe ’yan bindiga biyu, ta cafke wasu da ake zargi da satar babura
- IGP Disu ya buƙaci haɗin gwiwar jihohin Arewa maso Yamma wajen yaƙi da rashin tsaro
A cewar waɗanda suka miƙa wuyan, sansanin ya ƙunshi wasu ƙauyuka ko sassa da suka haɗa da Gari Ba’amfani, Mujiza, Guzuma, Sabon Tumbu, Yates Kura da Latimer. Sun ce ana ba mayaƙa makamai ne kafin su fita aikin kai hari, sannan su mayar da su ga shugabannin ƙungiyar bayan dawowarsu.
Sun kuma bayyana cewa ISWAP na kai hare-hare a sassa daban-daban na Borno, ciki har da Monguno, Marte, Ngoshe da Gamboru Ngala, da kuma wasu hare-hare a ƙetare kan iyaka zuwa Kamaru.
Sun ce ƙungiyar na samun kayayyakin gudanar da ayyukanta ta hanyar kai wa fararen hula da matafiya hari da kuma kwace kayan amfanin gona, yayin da sojojin Najeriya ke ci gaba da kai hare-haren ƙasa da sama tare da amfani da dabarun raunana ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da ƙarfafar waɗanda ke cikinsu su ajiye makamansu.