Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, ya yi kira da a ƙara haɗa kai tsakanin gwamnatocin jihohi da hukumomin tsaro domin magance matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma.

IGP Disu ya bayyana hakan ne a yayin taron tsaro na Arewa maso Yamma da aka gudanar a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, inda ya ce babu wata hukumar ts0aro ko gwamnati ko wata hukuma da za ta iya shawo kan matsalar tsaro a yankin ita kaɗai.

Ya ce yaƙi da matsalolin ’yan bindiga da satar mutane da yaɗuwar makamai da rikicin manoma da makiyaya da sauran laifuka na buƙatar musayar bayanan sirri tsakanin jihohi da haɗa ayyukan jami’an tsaro da ƙarfafa tsaron iyakoki da kuma haɗin gwiwar al’umma.

Babban Sufeton ya kuma jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya da al’ummomin yankin wajen samar da sahihan bayanan sirri da za su taimaka wajen hana aikata laifuka da kuma gano masu hannu a cikin ƙungiyoyin masu aikata laifuka.

IGP Disu ya yi gargaɗin kada a mayar da yaƙi da rashin tsaro zuwa batun ƙabila ko addini, yana mai cewa laifi ba shi da ƙabila, haka kuma ta’addanci ba shi da addini.

Ya buƙaci hukumomin tsaro su mayar da hankali wajen gano tare da gurfanar da ƙungiyoyin masu aikata laifuka da masu ɗaukar nauyinsu da masu samar musu da makamai da kuma masu taimaka musu, ba tare da la’akari da asalinsu ko ƙungiyarsu ba.

Taron, wanda Gwamnatin Jihar Zamfara ta shirya, ya haɗa gwamnoni da sarakunan gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro da masana da kungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna hanyoyin magance matsalolin tsaro da ke addabar Arewa maso Yamma.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *