Majalisar Zartarwa ta amince da sakin kudaden da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, EFCC, ta kwato domin tallafa wa bangaren ilimi a Najeriya.

Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai bayan taron Majalisar na ranar Laraba.

A cewar sa, kudaden zuwa Asusun Lamuni na daliban Najeriya (NELFUND) domin tallafa wa harkokin ilimin su.

Ministan ya bayyana cewa Majalisar ta kuma umarci Atoni-Janar na kasa da ya yi aiki tare da Ma’aikatar Ilimi wajen samar da hanyoyin da suka dace wajen saki da kuma amfani da kudaden.

Ya ce za’a samar da tsarin doka da ya dace domin tabbatar da cewa kudaden an yi amfani da su bisa ka’ida tare da tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen gudanar da su.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke kokarin kara samar da hanyoyin tallafa wa dalibai da kuma rage kalubalen rashin isassun kudade da ke damun bangaren ilimi.

Ta hanyar NELFUND, daliban manyan makarantu na Najeriya na samun damar neman lamunin kudade daga gwamnati, domin biyan kudaden karatu da sauran bukatun da suka shafi karatun su.

Majalisar ta ce samar da karin kudade ga wannan bangare zai taimaka wajen karfafa shirye-shiryen gwamnati na inganta damar samun ilimi da kuma tallafa wa matasa a fadin kasar.

Duk da haka, Ministan bai bayyana adadin kudaden da aka amince EFCC ta saki ba, ko kuma lokacin da za’a fara mika kudaden ba.

Ana sa ran Ma’aikatar Ilimi da Ofishin Atoni-Janar na kasa za su fitar da karin bayani kan yadda tsarin sakin kudaden zai Wakana, da yadda za’a yi amfani da su bayan kammala dukkanin tsare-tsare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *