Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a ranar Laraba ta amince da gyaran Dokar Lafiyar Ƙwaƙwalwa ta Ƙasa, domin cire laifin aikata yunƙurin kashe kai daga cikin laifukan da ake hukuntawa a Najeriya.

Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a mai, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan.

Ya ce manufar wannan garambawul ita ce rage kashe kai da kuma yunƙurin kashe kai da kashi 15 cikin 100 nan da shekarar 2030.

Da yake yi wa manema labarai bayani bayan taron Majalisar Zartaswa Ta Tarayya a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, Pate ya ce kashe kai na ci gaba da zama babbar matsalar lafiyar jama’a a Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

Ya yi nuni da bayanan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), waɗanda suka nuna cewa kashe kai na haddasa mutuwar sama da mutane 7,000 a kowace shekara a Najeriya, yayin da ake kiyasta cewa kusan mutane 300,000 ke yunƙurin kashe kansu a kowace shekara.

Ministan yace duk da girman matsalar, har yanzu yunƙurin kashe kai laifi ne a ƙarƙashin wasu tsoffin dokokin da aka gada daga zamanin mulkin mallaka, musamman Sashe na 327 na Dokar Penal Code da Sashe na 231 na Criminal Code.

A cewarsa, waɗannan dokoki suna kallon mutanen da ke cikin matsananciyar damuwa ta ƙwaƙwalwa a matsayin masu laifi maimakon mutanen da ke buƙatar kulawa da taimako.

Ya ce irin wannan tsarin doka na hana mutane neman taimakon da suke buƙata, kuma ya ci karo da Dokar Lafiyar Ƙwaƙwalwa ta Ƙasa ta 2021, wadda ta tanadi kulawa, kariya da magani ga mutanen da ke cikin haɗarin cutar da kansu.

Farfesa Pate ya ce hakan ya haifar da rashin daidaito tsakanin manufofin lafiyar ƙwaƙwalwa da tsarin shari’ar Najeriya.

Da yake bayyana dalilin da ya sa ake son sauya dokar, ministan ya ce matakin yana nuna sauyin fahimta daga kallon mutumin da ya yi yunƙurin kashe kansa a matsayin mai laifi zuwa kallonsa a matsayin wanda ke buƙatar kulawa da tallafi saboda matsalar lafiyar ƙwaƙwalwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *