Wasu ake zargin ’yan daba ne sun kai hari kan ayarin motocin Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, a ranar Laraba, jim kaɗan bayan ya ziyarci fadar Ataoja na Osogbo, Oba Jimoh Oyetunji.

Lamarin ya jawo musayar wuta tsakanin maharan da jami’an tsaron gwamnan.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an kwashe kusan minti 12 zuwa 15 ana harbe-harbe tsakanin jami’an tsaron gwamnan da maharan.

Adeleke ya isa fadar Ataoja da misalin ƙarfe 3:15 na rana, tare da ayarin motoci kusan 20, bayan ya bar hedikwatar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ke Osogbo, inda aka ba shi Takardar Shaidar Nasara (Certificate of Return) bayan sake zaɓensa a matsayin gwamnan jihar.

Wani ganau Ganau ya ce Adeleke ya riga ya bar ɗakin taron ta wata ƙofa da aka ware domin sarki da matansa kafin aka fara jin karar harbe-harbe.

Lamarin ya jawo fargaba da firgici a yankin, inda ’yan kasuwa da sauran mazauna yankin suka gudu daga wuraren kasuwancinsu domin neman mafaka yayin da ake ta harbe-harbe.

Da aka tuntubi Kwamishinan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Jihar Osun, Kolapo Alimi, ya tabbatar da faruwar harin.

Alimi ya ce jami’an tsaron gwamnan sun yi nasarar dakile maharan, kuma babu wanda ya rasa ransa ko ya ji rauni a lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *