’Yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja, a wani mataki na rage tashin hankali da tabbatar da gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin lumana.
An gudanar da bikin rattaba hannun ne a ranar Talata 18 ga Agusta 2026, ƙarƙashin jagorancin kwamitin zaman Lafiya na ƙasa tare da haɗin gwiwar cibiyar Kukah Centre.
Taron ya zo ne a daidai lokacin da jam’iyyu ke shirin fara kamfen ɗinsu a hukumance, gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai ɗan takarar jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, wanda Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya wakilta da ɗan takarar jam’iyyar NDC, Peter Obi, da ɗan takarar AAC, Omoyele Sowore, da sauran masu ruwa da tsaki kan harkokin zaɓe da suka haɗa da INEC, da jami’an tsaro da sauransu.
- Taron lacca da Karrama wasu Muhimman mutane na shekara -shekara na Jaridar Blueprint.
- NDLEA ta yi kamun Hodar Iblis mafi nauyi a tarihin kafuwar ta
- Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa a taron bada lambobin girma na Blueprint karo na 8.
A jawabinsa kafin bikin, Peter Obi ya yi kira ga ’yan siyasa da su gudanar da kamfen bisa batutuwan da suka shafi rayuwar ’yan Najeriya, maimakon amfani da kalaman da za su iya haifar da tashin hankali.
Obi ya ce bai kamata a samu wani ɗan Najeriya da zai rasa ransa saboda zaɓe ba, yana mai cewa ’yan siyasar da ke neman shugabanci ya kamata su kasance abin koyi wajen ɗabi’a da gudanar da kamfen.
Ya kuma bayyana cewa idan ɗan takara ko jam’iyya ta karya yarjejeniyar zaman lafiyar, hukuncin ƙarshe ya kamata ya fito daga hannun masu zaɓe, ta hanyar ƙin zaɓar irin waɗannan ’yan siyasa.
Yarjejeniyar zaman lafiya ta zo ne bayan ƙalubalen tashin hankalin da aka gani a wasu sassan ƙasar a lokacin shirye-shiryen zaɓe, ciki har da rikice-rikicen da suka faru a yayin zaɓen gwamnan Osun na baya-bayan nan.
Kwamitin, wanda aka kafa a shekarar 2014 da manufar rage barazanar rikicin siyasa, na amfani da irin wannan yarjejeniya wajen ƙarfafawa ’yan takara da jam’iyyu su mutunta tsarin dimokuraɗiyya tare da neman mafita cikin lumana idan aka samu sabani kan sakamakon zaɓe.
Sai dai bikin na bana ya fuskanci suka daga wasu ’yan siyasa.
Ɗan takarar AAC, Omoyele Sowore, ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani abu da zai iya zama bikin al’ada kawai idan ba a samar da ingantaccen tsarin da zai hukunta masu karya alkawuran ba.
Yarjejeniyar ta kasance ɗaya daga cikin muhimman matakan da ake sa ran za su taimaka wajen tabbatar da cewa kamfen ɗin 2027 ya kasance cikin lumana, yayin da ’yan Najeriya ke kallon ’yan takara da hukumomin zaɓe domin ganin an gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci da tsaro.