Hukumar Yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta ce jami’anta sun kama kunshin hodar iblis mai nauyin kilogiram 184.5, a hannun wani kamfanin aikewa da saƙonni.
Hukumar ta bayyana wannan nasara a matsayin kamu mafi girma da ta taɓa yi a tarihin kafuwar ta, wadda ƙimar ta ta kai dalar Amurka miliyan 27.7, kwatankwacin naira miliyan 39
Da yake jawabi yayin wani taron manema labarai a birnin Legas ranar Talata, Shugaban NDLEA, Buba Marwa, ya ce hukumar na tsare da mutane biyu da ake zargi da hannu a safarar.
Waɗanda ake zargi sun haɗa da Afolabi Kazeem Micheal da aka fi sani da “KC Luxury” wanda aka kama a filin jirgin saman Legas yayin da yake ƙoƙarin tserewa daga ƙasar.
Sai wakilin kamfanin aika saƙonnin mai suna Lawal Kehinde, wanda shi kuma bangaren gudanarwar kamfanin aika saƙonnin ya kawo shi gaban hukumar ba tare da wata damuwa ba.
Marwa ya ce an samu kuɗaɗen ƙasashen ƙetare da suka haɗar da Yuro dubu 7,750, da Fam ɗin Ingila dubu 2,800, sai kuma Naira dubu 100,000, da wasu kaya masu daraja. Haka kuma an gano motocin al’alfarma a gidan sa da ke yankin Banana Island a Ikoyi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tun a ranar 13 ga watan Agustan shekarar 2026 ne hukumar ke bibiyar wanda ake zargin, biyo bayan samun bayanan sirrin da ke nuna yana shirin tserewa daga ƙasar.
Hukumar ta ce ana amfani da Nijeriya ne a matsayin wata turbar safarar miyagun ƙwayoyi zuwa ƙasar Ingila, da sauran ƙasashen Turai, da na Asiya.
Ko a ranar litinin 18 ga wata, reshen hukumar a jihar Kano ya bayyana kama wata Motar Bas maƙare da miyagun kwayoyi, kamun da hukumar ke cewa ya tabbata ne sakamakon samun bayanan sirri daga jama’a.