Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) reshen jihar kano ta samu nasarar cafke wata motar safa maƙare da miyagun kwayoyi, da ƙimar su ta haura naira Miliyan 370.
Wani ɓangare na wannan miyagun kwayoyi na daga cikin kayan da jami’an hukumar suka samu nasarar kamawa a yayin wani sumame.
- Kebbi – Gwamna Nasir Idris ya maye gurbin mataimakin sa da kwamishina
- FCTA na ɗaukar matakan magance ambaliyar ruwa a wasu sassan Abuja – Olayinka
- Kano – Almajirai huɗu sun mutu bayan cin gurɓataccen abinci
A cewar mai magana da yawun Hukumar a jihar Kano Sadiq Muhammad, nasarar ta samu ne sakamakon ƙoƙarin jami’an hukumar wajen daƙile safarar miyagun ƙwayoyi da hana shigar da su cikin al’umma.
An bayyana cewa Tramadol na daga cikin magungunan da ake yawan amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba, musamman a tsakanin matasa, lamarin da ke haifar da matsalolin lafiya da zamantakewa.
NDLEA ta jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukan bincike da kama masu safarar miyagun ƙwayoyi a sassa daban-daban na ƙasar domin kare lafiyar jama’a da rage yaduwar miyagun ƙwayoyi.