Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris, ya ajiye mataimakin sa, Umar Tafida, tare da ɗauko tsohon kwamishinan kuɗin jihar Ibrahim Augie a matsayin wanda za su yi takara tare a babban zaɓe na shekarar 2027.
- FCTA na ɗaukar matakan magance ambaliyar ruwa a wasu sassan Abuja – Olayinka
- Kano – Almajirai huɗu sun mutu bayan cin gurɓataccen abinci
- Cardoso, Ojulari, Tantita za su karɓi lambobin yabo na Blueprint Newspapers
Kamfanin dillancin labarai na RFI ya ruwaito wata sanarwa dake cewa Gwamnatin Kebbi ta ce Idris ya sauya abokin takarar tasa ne bawai saboda ya gaza ba, sai dan irin ƙararrakin da aka shigar gaban kotu bayan zaɓen 2023 wanda ya haɗa da mataimaikin nasa Umar Tafida da wasu masu ruwa da tsaki.
Hakan ne yasa ƙwararru a fannin shari’a suka bashi shawarar sauya mataimakin nasa a takarar gwamna da zai sake fitowa ƙarƙashin jam’iyyar APC, saboda gudun samun matsala.