Ambaliyar ruwa ta sake addabar wasu sassan Abuja sakamakon ruwan sama mai ƙarfi, lamarin da ya sake jawo hankalin jama’a kan yadda toshe hanyoyin ruwa da sauya wasu wuraren da aka ware domin korewar birni ke ƙara tsananta matsalar.

Ambaliyar ta shafi yankunan Wuse 2 da Mabushi da Lugbe da Gwarinpa da Wuye da Gudu da Nyanya da Asokoro da Maitama da wasu wurare, inda ruwa ya mamaye hanyoyi tare da jefa wasu mazauna da masu ababen hawa cikin wahala.

Wasu mazauna Abuja sun danganta matsalar da yadda ake gina gine-gine a wuraren da aka ware domin shakatawa kusa da hanyoyin ruwa, lamarin da suke cewa yana rage damar ƙasa na tsotse ruwan sama tare da ƙara yawan ruwan da ke gudana a kan tituna.

Haka kuma, zubar da robobi da leda da shara da sauran tarkace a magudanan ruwa na daga cikin abubuwan da ke hana ruwa samun hanyar wucewa yadda ya kamata.

Hukumomin kula da agajin gaggawa sun ce sun fara tantance wuraren da ambaliyar ta shafa tare da duba irin taimakon da mazauna ke buƙata.

Hukumar NEMA da FCT FEMA sun gudanar da aikin tantancewa a Wuse, Mabushi da wasu wuraren da ambaliyar ta shafa domin gano barnar da aka samu a gidaje da tituna da wuraren kasuwanci da sauran muhimman ababen more rayuwa.

Hukumomin sun kuma buƙaci mazauna wuraren da ke fuskantar barazanar ambaliya da su kasance cikin shiri, su guji shiga hanyoyin da ruwa ya mamaye, tare da bin shawarwarin jami’an tsaro da hukumomin agajin gaggawa.

Hukumar FEMA ta kuma gargadi masu ababen hawa da kada su yi ƙoƙarin tuƙi cikin ruwan ambaliya, saboda ba a san zurfin ruwan ba kuma ana iya samun ambaliyar bazata da za ta iya kwashe mutane ko motoci.

Hukumomin sun kuma bukaci mazauna Abuja da su riƙa tsaftace magudanan ruwa, su guji gina gine-gine a kan hanyoyin ruwa, tare da kai rahoton duk wani gini ko ci gaban da ke hana ruwa bin hanyarsa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *