Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) da Olayemi Cardoso; Babban Daraktan Gudanarwa na Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC Ltd), Injiniya Bashir Bayo Ojulari; da kamfanin Tantita Security Services Limited, na daga cikin fitattun mutane da ƙungiyoyin da za a karrama a bikin lambar yabo na shekara-shekara na Blueprint Newspapers, wanda zai gudana a ranar Talata, 18 ga Agusta, 2026.
Taron, wanda za a gudanar da taron ne a ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre, Abuja, zai haɗa manyan jami’an gwamnati, shugabannin siyasa, ’yan kasuwa da shugabannin kamfanoni, ƙwararrun harkokin tsaro, jami’an diflomasiyya, malamai, wakilan ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki.
Cardoso zai karɓi Kyautar mafi dorewa a harkokin kula da Dokokin Harkokin Kuɗi, saboda irin jagorancin da yake yi a babban bankin ƙasar da kuma ƙoƙarinsa na ƙarfafa tsarin tafiyar da harkokin kuɗi, daidaiton tsarin kuɗi da sa ido kan dokokin bankuna a Najeriya.
- Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo ya yi murabus
- Wani Fasto ya karrama wani malamin Addinin Musulunci a Najeriya
- Adeleke: Har yanzu Oyebamiji bai taya ni murna ba
Za kuma a baiwa Ojulari Kyautar Jagorancin Kamfani (Corporate Leadership Award) saboda yadda yake jagorantar NNPC da kuma gudummawar da yake bayarwa wajen sake fasalin kamfanin makamashin ƙasa domin samun ƙarin inganci, gasa, riƙon amana da kyakkyawan tsarin kasuwanci.
Kamfanin Tantita Security Services Limited kuwa zai karɓi Kyautar Kwarewa wajen Sa-Ido kan Tsaro (Outstanding Security Surveillance Award) saboda gudummawar da yake bayarwa wajen sa ido da kare muhimman ababen more rayuwa na harkokin mai da gas a Najeriya.
Wadannan lambobin yabo na daga cikin ƙoƙarin Blueprint Newspapers Limited na karrama mutane, hukumomin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu waɗanda ayyukansu suka samar da gagarumar gudummawa a fannonin shugabanci, kuɗi, gudanar da kamfanoni, tsaro da ci gaban ƙasa.
Kafin bikin bayar da lambobin yabon, za a gudanar da wata lacca ta jama’a mai taken “Matsalolin Tsaro da Ingancin Zaɓen Najeriya na 2027”, wadda Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), zai gabatar.
Ana sa ran laccar za ta duba alaƙar da ke tsakanin tsaron ƙasa da gudanar da sahihin zaɓe, yayin da Najeriya ke shirin babban zaɓen shekarar 2027.
Haka kuma, ana sa ran za a karrama wasu fitattun ’yan Najeriya, gwamnatocin jihohi, hukumomin gwamnati da kamfanoni a fannoni daban-daban yayin bikin.