Wani malamin addinin Kirista da ke zaune a Kaduna, Fasto Dr. Yohanna Buru, ya girmama wani malamin Musulunci, Sheikh Usman Mohammed Mai-Mota (Gwalli), saboda sadaukar da fiye da shekaru hamsin wajen koyar da ilimin Musulunci da horar da dubban matasa.
Fasto Buru, wanda shi ne Babban Jagoran Ikilisiyar Christ Evangelical and Life Intervention Ministry, ya jagoranci wata tawaga ta malamman Kirista zuwa makarantar Sheikh Usman, inda suka miƙa masa lambar yabo domin nuna godiya ga gudunmawarsa ga ilimin Musulunci da ci gaban al’umma.
Da yake jawabi a yayin ziyarar, Fasto Buru ya bayyana cewa Sheikh Usman ya shafe fiye da shekaru 50 yana koyar da Al-Ƙur’ani, Hadisi, Tafsiri, Harshen Larabci da sauran fannoni na ilimin Musulunci ga yara da matasa daga sassa daban-daban na Arewacin Nijeriya.
Ya ci gaba da cewa da yawa daga cikin waɗanda suka yi karatu a makarantar malamin sun zama malamman Musulunci, malamman koyar da Harshen Larabci, da lakcarori a makarantu, cibiyoyi, da majalisun ilimi daban-daban a faɗin ƙasar.
A cewar Fasto Buru, wannan karramawa an yi ta ne domin ƙarfafa wa Sheikh Usman gwiwar ci gaba da ƙoƙarinsa na ilimantar da matasa duk da tsufan da ya yi.
- Yadda Kamaru ta lashe kofin Gasar WAFCON ta 2026 da ci 3-0 akan Malawi
- Adeleke: Tinubu ya taya ni murna, amma har yanzu ina jiran kiran Oyebamiji
- Adeleke ya ƙara jaddada goyon bayan sa ga Tinubu a Zaɓen
Ya bayyana gudunmawar malamin a matsayin babbar hidima ga ɗan adam, inda ya jaddada cewa mutanen da suka sadaukar da rayuwarsu wajen ilimantar da dubban matasa sun cancanci a karrama su kuma a ƙarfafa musu gwiwa.
“Mun zo ne domin mu girmama shi, mu nuna godiya ga gudunmawarsa, sannan mu gode masa kan hidimar da ya yi wa ɗan adam ta hanyar ilimin Musulunci,” in ji Fasto Buru.
Ya ƙara da cewa karramawar tana ɗaya daga cikin ƙoƙarin inganta zaman lafiya da ƙarfafa dangantaka tsakanin Musulmi da Kiristoci a Jihar Kaduna.
Fasto Buru, wanda aka karrama a lokacin Makon Ƙarfafa Zaman Lafiya da Haɗin Kan Addinai na Majalisar Ɗinkin Duniya a shekarar 2022, ya ce aikin Sheikh Usman ya taimaka wajen samar da tsara-tsarar malamman Musulunci da masana.
Tawagar ta bayyana cewa binciken da aka yi ya nuna cewa Sheikh Usman ya horar da matasa fiye da 10,000, waɗanda da yawa daga cikinsu a yanzu suke aiki a matsayin malamman Larabci, malamman Musulunci, da lakcarori a sassa daban-daban na Arewacin Nijeriya.
Shi ma da yake jawabi, Fasto Emmanuel John ya bayyana gudunmawar Sheikh Usman a matsayin abin azo a gani, inda ya ce sadaukarwar da ya yi wajen ilimantar da matasa ilimin Musulunci ta bar gurbin da ba za a manta da shi ba.
Ya ce ziyarar ba wai kawai domin girmama malamin ba ce, har ma domin ƙarfafa girmama juna da kyakkyawar fahimta tsakanin Kiristoci da Musulmi.
“Mun zo ne domin mu yaba wa gudunmawarsa ta azo a gani da kuma ƙarfafa dangantaka tsakanin Musulmi da Kiristoci, da nufin inganta zaman lafiya, haɗin kai, da kyakkyawar fahimta a jihar,” in ji shi.
Da yake maida jawabi, Sheikh Usman Mohammed Mai-Mota (Gwalli) ya nuna godiyarsa ga tawagar Kiristocin bisa wannan karramawa, inda ya bayyana ita a matsayin lambar yabo ta farko da ya samu a shekarunsa fiye da 50 na koyarwa.