A karon farko, kasar Kamaru ta lashe Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka na Mata (WAFCON) bayan ta doke Malawi da ci 3-0 a wasan karshe na 2026 da suka buga a Rabat, dake Marokko.

‘Yan matan Kamaru sun zura kwallaye ukun ne a rabin farko na wasa. Marie Ngah Manga ta zura kwallaye biyu sannan kuma Naomi Eto ita ma ta ci wani kyakkyawan kwallo mai ban sha’awa.

Sau uku Kamaru ta ke kammala Gasar WAFCON a matsayi na biyu a tarihi, yayin da wannan shi ne karo na farko da Malawi ta halarci gasar.

Da farko, Kamaru ba ta samu tikitin shiga gasar wadda kasashe 12 ke fafatawa ba, sai da Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka, CAF, ta yanke shawarar kara yawan kasashen zuwa 16, wanda hakan ya ba su dama ta biyu.

A wasanni biyar da suka gabata wadda Kamaru ta buga a gasar, ta zura kwallaye 4 kawai, kuma galibin nasarorin da ta samu ya samo asali ne daga bajintar mai tsaron ragar ta, Michaely Bihina, wadda ta ke taka leda a kungiyar Benfica.

Amma a wasan karshe, ‘yan wasan Kamaru ba su bukaci taimakon mai tasaron ragar da yawa ba, saboda ‘yan wasan gaban kasar sun fito da karfin su lokacin da ya fi dacewa.

Bayan sun buga wasan karshe sau 3 a baya (2004, da 2014 da kuma 2016), a yanzu, Kamaru ta daga kofin a karon farko. Ta zama kasa ta hudu da ta taba lashe Gasar WAFCON, inda ta bi sahun Najeriya, Equatorial Guinea da Afirka ta Kudu a wannan dandali na musamman.

A gefe guda kuma, Malawi ta bayar da mamaki ganin cewa wannan ne karon farko da ta halarci gasar a tarihi, inda ‘yan wasa ‘yan uwan juna, Temwa da Tabitha Chawinga suka yi fice.

Su biyun, sun zura kwallaye 9 daga cikin kwallaye 13 da tawagar wadda ake mata lakabi da Scorchers, ta ci a gasar baki daya. Sannan sun taimaka wajen fitar da manyan tawagu irin su Najeriya da Ghana a hanyarsu na zuwa wasan karshe.

Ko da yake za su ji bakin cikin rashin lashe kofin, to amma samun tikitin buga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata na bana mai zuwa a Brazil har yanzu nasara ce mai ban mamaki ga ‘yan wasan wanda za suyi alfahari da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *