A karon farko Najeriya ta kasa samun gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata bayan da Afirka ta Kudu ta doke ta da ci 2-1 a wasan neman gurbin shiga gasar, wanda aka buga a Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka ta Mata (WAFCON) ta 2026 a daren ranar Alhamis.
Tawagar Super Falcons wadda ita ce da matsayi na 1 a Afirka ta shiga gasar WAFCON da ke gudana a Marokko a matsayin wadda ake sa ran za ta kare kofinta, amma an fitar da ita a wasan kwata-fainal da ta buga da Kamaru. Sannan kuma ta sha kashi a hannun Malawi a wasan matakin rukuni.
Tun bayan baiwa tawagu 4 da suka kai wasan kusa da na ƙarshe gurbin kai tsaye zuwa Gasar Duniya ta bana, ‘yan wasan na Justin Madugu suka sake samun wata dama ɗaya ta ƙarshe don ci gaba da fatan zuwa Brazil, inda duk wadda ta yi nasara a wannan wasa da suka buga a Casablanca za ta tsallaka matakin gaba na wasannin neman gurbin shiga gasar Duniya.
- PSG ta lashe kofin Super Cup bayan doke Aston Villa
- WAFCON 2026: Malawi ta kai wasan karshe bayan lallasa Aljeriya
- Akwai bukatar NFF tayi nazari kan koma bayan da take samu-Masharhanta
Kwallaye biyu da Thembi Kgatlana da Refiloe Jane suka ci a rabin wasa na biyu sun ishi Banyana Banyana samun nasara, duk da fargaban da ya faru a ƙarshen wasan lokacin da aka baiwa Jane, jan kati saboda ta taba ƙwallo da hannu a cikin gidan ta.
Christy Ucheibe ta ci wa Najeriya bugun fenareti a minti na 93 don karawa wasan za fi a ƙarshen lokaci. Sannan ma mai tsaron ragar Afirka ta Kudu, Kaylin Swart, wadda ta kasance jarumar wasan, ta yi ceto mai ban mamaki da ƙafafunta don hana Michelle Alozie cin wani kwallo a bugun ƙarshe na wasan.
Najeriya ta buga dukkan Gasa 9 na Cin Kofin Duniya ta Mata tun da aka fara a kasar China a shekarar 1991.
A yanzu, Afirka ta Kudu wadda ta lashe Gasar WAFCON ta 2022 za ta bi sahun kasar Ghana a wasannin shiga Gasar Duniya tsakanin kasashe daga nahiyar, bayan da Black Queens din suka farfado daga baya suka doke Ivory Coast da ci 2-1 a ranar Alhamis.