A yammacin ranar, Laraba, kasar Malawi ta samu tikitin shiga wasan ƙarshe na gasar cin Kofin Mata na Nahiyar Afirka (WAFCON) ta 2026, bayan ta doke Aljeriya.

Tawagar na ‘yam matan Malawi wadda ake musu lakabi da (The Scorchers) sun doke Aljeriya da ci 3-1 a wasan kusa da na ƙarshe na WAFCON, wanda ake buga wa a Marokko.

Tabitha Chawinga ta ci kwallaye 2, yayin da ‘yar’uwarta Temwa Chawinga ta ci kwallo ɗaya. Wadannan kwallaye su suka baiwa Malawi nasara a kan ƙasar Arewacin Afirka.

Ikram Adjabi ce ta ci ƙwallo ɗaya tilo ga Algeria a rabi na biyu.

Sakamakon wasan ya nuna cewa Malawi za ta fuskanci wadda za ta yi nasara tsakanin Kamaru da Marokko a wasan ƙarshe na WAFCON ranar Lahadi.

A gefe guda kuma, Aljeriya za ta fuskanci wadda ya sha kashi a wasan Kamaru da Marokko a ƙarshen wannan mako don neman matsayi na uku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *