Cristiano Ronaldo ya angwance da budurwarsa da suka dade suna soyayya, Georgina Rodriguez, a wani taro  da aka yi a ƙasar Portugal.

Ma’auratan, waɗanda suka kasance tare tun shekarar 2016 bayan haɗuwar su a Madrid, daga nan suka wallafa hoton yatsun su da zoben aure a Instagram.

Ronaldo mai shekaru 41, ya yi auren ne kwanaki 4 kawai kafin ƙungiyarsa ta Al Nassr ta fara kakar wasan Saudi Pro League ta 2026-27.

An yi auren ne a Cascais dake gaɓar Teku mai nisan mil 20 zuwa yamma da babban birnin Portugal Lisbon, tare da halartar ‘ya’yansu biyar.

Ronaldo ya ci kusan kwallaye 1,000 a cikin rayuwar sa ta ƙwallo yayin da ya buga wa Sporting, Manchester United, Real Madrid, Juventus, Al Nassr da tawagar ƙasar Portugal.

Kwanan nan ya buga Gasar cin Kofin Duniya ta shida, inda ya zama daya da Lionel Messi na Argentina a matsayin ‘yan wasan da suka fi buga wasannin Gasar cin Kofin Duniya na maza.

A farkon wannan bazara, Ronaldo ya tabbatar da cewa ya gama buga wasansa na ƙarshe na Gasar cin Kofin Duniya – amma ya ce ba zai yanke “shawara ta gaggawa” ba, game da ko ya gama buga wa ƙasar sa wasa gaba ɗaya.

“Ina cikin baƙin cikin fita daga Gasar cin Kofin Duniya haka,” in ji shi.

Ronaldo ya ce zai ci gaba da yin tunani akan makomar bugawa ƙasar sa yayin da yake baiwa iyalan sa kulawa a ɓangare guda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *