A karon farko, Arsenal ta dawo wasa a filin ta na Emirates tun bayan da ta lashe Gasar Firimiyar Ingila, sai dai Dortmund ta lallasa ta da ci 3-2 inda ta ɗaga kofin Emirates akan ta.
kafin wannan wasa, kocin Arsenal, Mikel Arteta ya yi ƙorafi kan irin raunin da tsaron bayan kungiyar ke da shi a yanzu biyo bayan shan kaye a hannun Real Betis a wasan da suka buga ranar Laraba, inda aka doke Gunners ɗin da ci 1-3.
Arsenal ta samu damarmakin doke Dortmund a wasan amma ‘yan wasan gaban ta sun ɓarar da damarmakin.

-
Yadda Marmoush ya zura ƙwallo biyu yayin da Man City ta doke Atletico
-
WAFU B U20: Flying Eagles na fatan rama abinda Burkina Faso ta yi mata —- Maikaba
-
WAFCON: Marokko ta doke Afirka ta Kudu 2-1
Sabon ɗan wasan da Arsenal ta saya, Tzolis, ya taka muhimmiyar rawar gani inda ya samu Fenaretin da aka baiwa Gyokeres ya buga kuma ya zura ƙwallon a raga a minti na 69.
Kafinnan, Ethan Nwaneri shi ya fara ci wa Arsenal ƙwallo a minti na 54.
Dortmund ta ci ƙwallayen ta ne ta hannun Samuele Inacio a minti na 7 da fara wasa. Sannan kuma Konstantinos Karetsas ya ƙara wani ƙwallon a minti na 29. Daga bisani Joane Gadou ya ci nasa ƙwallon a minti na 58.
Kafin fara wasan, Arsenal ta gabatar da sabon ɗan wasan da ta siya, Bruno Guimaraes, ga magoya baya a filin Emirates.
Arsenal mai riƙe da kambun Firimiyar Ingila za ta kara da Manchester City wadda ta lashe Gasar FA Cup akan Chelsea ranar Lahadi, 16 ga watan Augusta.