Tawagar Atlas Lioness, mai fatan Lashe Kofin WAFCON a karo na farko, tana kara tashe a harkar kwallon kafa a Nahiyar Afrika

Tawagar Atlas Lionesses ta kasar Marokko ta lallasa Banyana Banyana ta Afirka ta Kudu a wasan kwata-fainal na Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka ta Mata (WAFCON) ta 2026 a wasan kwata-fainal da suka buga a daren ranar Asabar.

Wannan nasara ba kawai ta tura Atlas Lionesses zuwa wasan kusa da na karshe ba ne, ta kuma ba ta damar samun tikitin zuwa Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata da za a yi a Brazil a shekarar 2027.

‘Yan wasan na Marokko ne suka fara cin kwallo sannan Hanan Ait El Haj ta kara daya a minti na 51 ta hangar bugun fanareti

A minti na 67 kuma Thembi Kgatlana ta farke wa Afirka ta Kudu kwallo daya, damarın da ya sa ‘yan basan Bayana Bayana fatan farkewa gaba daya.

Sai dai Zakanyoyin na Atlass sun rike wuta har aka hura usar din karshe.

A shekarar 2022 ne dai tawagar Atlas Lionesses ta kai wasan karshe na Gasar WAFCON a karo na farko, rawar da takę fatan sake takawa a wannan karon da ma fatan lase kofin a karo na farko.

A nata wasan, Algeria ta nuna juriya da kuma jarumta ta hanyar farfadowa daga baya, yayin da ta doke Ivory Coast da ci 2-1 a wasan kwata-fainal da suka buga a ranar Asabar.

Sannan ita ma Aljeriya ta samu gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata ta 2027 a kasar Brazil.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *