Real Madrid ta sanar cewa Vinicius Jr. ya sabunta kwantiragin da zai ajiye shi har zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2032.

Madrid ta sanar da hakkan ne ranar Alhamis, 6 ga watan Augustan 2026.

Kwantiragin sa na baya daman zai kare ne a watan Yunin 2027, yayin da hakan ya janyo cece-kuce game da makomarsa a kungiyar.

Vinicius dan asalin kasar Brazil mai shekaru 26, tun komawarsa Madrid daga Flamengo a 2018, ya buga wasanni 375, inda ya ci kwallaye 128, kuma ya lashe kofuna 14 ciki har da Gasar Zakarun Turai guda 2 da kuma La Liga 3.

A shekara ta 2024, Vinicius ya lashe kyautar Gwarzon dan wasan FIFA na maza kuma ya zo na biyu a zaben Ballon d’Or bayan Real ta lashe La Liga da Champions League.

Kafin sabunta kwantiragin, an danganta Vinicius da komawa kungiyar Arsenal da ke buga Gasar Firimiyar Ingila. Amma sabon kwantiragin ya kawo karshen jita-jitar canza shegar na sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *