Tawagar ‘yan ƙasa da shekaru 20 ta Najeriya, Flying Eagles, sun samu gurbin wasan ƙarshe na Gasar WAFU B U20 ta 2026, bayan samun nasara mai ban sha’awa da ci 4-3 a bugun fenareti akan mai masaukin baƙi Ivory Coast.

Wasan wadda aka buga da yammacin ranar Laraba, an tashi ci 2-2 bayan ƙarin lokaci wanda hakan ya tilasta zuwa bugun fenareti.

A mintuna na 16 da fara wasa ɗan wasan Ivory Coast, Kaita ya ci ƙwallo ta farko da ta ɗaura masu masauƙin baƙi kan gaba da ci 1-0, sannan suka ci gaba da matsa wa Flying Eagles lamba amma mai tsaron raga, Lawani, ya buge ƙwallaye ma su ban mamaki da dama domin baiwa Najeriya ƙwarin gwiwa a karawar.

Kyaftin ɗin Flying Eagles, Habila Simeon ya farke ƙwallon da aka ci Najeriya a minti na 67 yayin da wasan ya dawo ci 1-1. Duk da ɓangarori biyun sun samu damarmaki na cin ƙwallo, to amma ba a ƙara ci ba har aka tafi ƙarin lokaci da ci 1-1.

A minti na 93,Aliyu Abubakar, ya ɗaura Flying Eagles kan gaba da ci 2-1 a farkon ƙarin lokacin. Kazalika, a minti na 100, Gift Subi yayi ƙokarin ƙara ta 3 amma harin da ya kai ya tafi gefe.

Ivory Coast sun mayar da martani nan take inda suka zura ƙwallo, wasan ya koma ci 2-2 kafin ƙarshen rabin farko na ƙarin lokaci.

Wasan ya ƙare ne da ci 2-2 bayan ƙarin lokaci, inda aka ta fi bugun fenareti. Nan ne Flying Eagles suka samu nasara a karawar da ci 4-3.

Wannan nasara ta tura Najeriya zuwa wasan ƙarshe na gasar WAFU B U20 ta 2026, inda za su yi yunƙurin kare kambun su da kuma samun tikitin zuwa Gasar cin Kofin Afirka ta U20 ta bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *