Biyo bayan shan kaye a wasan farko, Super Falcons ta Najeriya ta ci gaba da nuna bajin ta yayin da ta yi wa tawagar ‘yam matan ƙasar Masar wadda ake yi wa laƙabi da The Cleopatras wankin babban bargo da ci 6-2 a Gasar cin Kofin Mata na Nahiyar Afirka (WAFCON), ta 2026.
Sun buga wasan ne a daren ranar Laraba a filin wasa na Stade Moulay Hassan dake ƙasar Marokko.
Taurarin ‘Yan wasannin da suka ci wa Najeriya ƙwallayen sun haɗa da Asisat Oshoala, da Gift Monday, da Uchenna Kanu, da Christy Ucheibe, da Kyaftin din tawagar, Rasheedat Ajibade, da kuma Joy Omewa.

-
An tarbi Salah kamar jarumi kafin komawarsa Trabzonspor
-
Cristiano Ronaldo ya kalli wasan da ƙungiyar sa ta lallasa Al Nassr
-
Infantino ya gudanar da taron Gaggawa a Morocco
A ɓangaren ƙasar Masar kuwa, ‘yar wasa Nadine Ghazi ce ta zura duka ƙwllaye biyun da ƙasar ta samu yayin fafatawar. Har ila yau, Masar ta kammala wasan rukuni ba tare da yin nasarar ko da wasa guda ba.
Wannan nasara ta ƙara wa Najeriya wadda ke riƙe da kofin kuma zakarar gasar har sau 10 ƙwarin gwiwar fuskantar tsohuwar abokiyar hamayyar ta wato Kamaru a wasan kusa da na ƙarshe da za su buga ranar Lahadi.
Kamaru ta tsallaka zuwa wannan matakin ne yayin da ta jagoran ci rukunin D, bayan ta doke Ghana da Mali, za ta kuma buga da Cape Verde a wasan su na rukuni na ƙarshe.

Fafatawar da Najeriya za ta yi da Kamaru zata sake sabunta hamayyar da ta daɗe tsakanin ƙasashen biyu, wadda ta yi nasara za ta samu tikitin zuwa Gasar cin Kofin Duniya na Mata ta 2027 a Brazil kai tsaye.