Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, da Hafsan Hafsoshin Sojin ƙasar, Janar Asim Munir, za su kai ziyara ƙasar Saudiyya daga ranar 6 zuwa 8 ga watan Agusta, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta bayyana a ranar Alhamis

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Pakistan, Tahir Andrabi, ya ce ziyarar za ta gudana ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙarin tashe-tashen hankula a yankin Tekun Fasha.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Pakistan na ci gaba da taka rawa wajen shiga tsakani domin kawo ƙarshen rikicin da ya ɓarke tsakanin Amurka da Iran, rikicin da ya shafi wasu ƙasashen gabas ta tsakiya ciki har da Saudiyya

Ma’aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta kuma yaba wa ƙasar Oman,game da rawar da take takawa wajen warware matsalar da ta shafi mashigar ruwan Hormuz

A ranar Laraba, mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya bayyana cewa Iran da Oman sun cimma matsaya kan iyakokin zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar ruwan, kuma ana daf da kammala shirye-shiryen fitar da sanarwar haɗin gwiwa, matuƙar wasu ɓangarori na waje ba su tsoma baki ba

Sai dai Baghaei ya jaddada cewa ko da Iran da Oman sun cimma irin wannan yarjejeniya, hakan kaɗai ba zai tabbatar da cikakken tsaro a mashigar ruwa ba

Wasu majiyoyi sun ce yarjejeniyar da ake shirin ƙullawa tsakanin Iran da Oman za ta bai wa Tehran ikon kula da jiragen ruwa da ke shiga Tekun Fasha ta mashigar.

Wata majiya mai tushe daga Iran da wasu jami’ai biyu na yankin sun bayyana hakan a ranar Laraba, suna masu cewa wannan na ɗaya daga cikin sassaucin da aka taɓa yi wa Iran

Duk da wannan ci gaban da ake gani a tattaunawar, majiyoyin sun ƙaryata ikirarin Shugaban Amurka, Donald Trump, cewa an kusa cimma yarjejeniyar sake buɗe mashigar, sai dai  har yanzu akwai wasu muhimman batutuwa da dama da ba a kammala tattaunawa a kansu ba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *