Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce zai umarci dakarun Amurka da su dakatar da sabbin hare-hare kan Iran, yana mai cewa ƙawayen Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya sun cimma wasu muhimman ka’idojin yarjejeniya da za ta kawo ƙarshen yaƙin da ya shafe watanni biyar yana gudana.

Trump ya rubuta a wani saƙo da ya wallafa a kafar sada zumunta cewa yarjejeniyar da ake shirin cimma wa za ta ƙunshi “buɗe mashigar Hormuz gaba ɗaya cikin gaggawa, da kuma kawo ƙarshen barazanar nukiliyar Iran.”

Trump ya taɓa sanar da dakatar da hare-hare kan Iran sau da dama tun bayan da Amurka da Isra’ila suka kai hari kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, saidai fadan yaci gaba da dawowa.

Sai dai ko a karshen makon nan an jiyo wani janar na sojin Amurka dake jagorantar sojin kasar a faɗan da takeyi da Iran na cewa ba su da isassun makamai da za su ci gaba da kai hare hare a yakin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *