Babban kwamandan Amurka a Turai ya gargaɗi ma’ikatar tsaron Amurka Pentagon a asirce cewa ba su da isasshen ƙarfin ci gaba da kare Isra’ila daga hare-haren makamai masu linzami.
Jaridar The Washington Post ta ruwaito cewa Janar Alexus Grynkewich, shugaban rundunar sojin Amurka a Turai, ya shaida wa manyan jami’an Pentagon cewa idan ba a samar da ƙarin jirgin ruwa na yaƙi (Navy destroyer) ba, zai zama wajibi ya fifita kare ‘gidan’ Amurka kan Isra’ila.
- Jami’an Tsaron Nijar fiye da 10 sun mutu a harin Boko Haram a Diffa
- Mali: HRW ta zargi dakarun Africa Corps na Rasha da kashe fararen hula takwas
- Guinea da Gabon sun warware tsohuwar takaddamar dake tsakanin su
Gagarɗin na zuwa ne yayin da yaƙi na watanni biyar ke ƙara zafi bayan tattaunawar sulhu tsakanin Washington da Tehran ta rushe, inda rahotanni suka ce hare-hare babu ƙaƙƙautawa na ƙarar da makaman kariyar Amurka.
Rundunar Sojin ruwan ƙasar ta fuskanci ƙarin matsin lamba yayin da gwamnatin Trump ta ba da umarnin yi wa Iran ƙawanya sanadiyyar matakin da Tehran ta ɗauka na rufe mashigar Hormuz, lamarin da ya katse jigilar mai da kasuwancin duniya.
Jiragen yaƙin ruwan Amurka a gabashin tekun meditareiniyan sun daɗe suna taimakawa wajen kare Isra’ilal, inda suke amfani da ingatattun na’urar hango ababe da tsare-tsaren makamai masu linzami wajen kakkaɓo makamai masu linzamin da Iran da ‘yan Houthi na Yemen suka harbo.