Ƙasar Gabon da Equatorial Guinea sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen doguwar takaddamar da ta shafe shekaru da dama tsakaninsu kan wasu ƙananan tsibirai uku da ke cikin yankin teku.
Wannan ya biyo bayan hukuncin babbar kotun Majalisar Ɗinkin Duniya da ya baiwa Malabo nasara.
Ƙasashen biyu na yammacin Afirka sun kwashe shekaru suna takaddama kan tsibirin Mbanie mai fadin hekta 30, da kuma wasu ƙananan tsibirai biyu, Cocotiers da Conga tun farkon shekarar 1970
- Taron ƙungiyar ‘Yan Nijar ma zauna ƙasashen waje – wacce gudunmuwa hakan zai haifar ga tattalin arziki
- Nijar ta dakatar da kamfanonin dillancin siminti 36 kan zargin ɓoye shi
A watan Mayun shekarar da ta gabata, Kotun Ƙasa da Ƙasa (ICJ) da ke birnin Hague, wadda ke yanke hukunci kan rikice-rikicen da ke tsakanin ƙasashe, ta yanke hukuncin.
A wani taro da aka gudanar a hedkwatar Tarayyar Afirka (AU) da ke Addis Ababa, Ministan Harkokin Wajen Equatorial Guinea, Simeon Oyono Esono Angue, da shugaban Majalisar Tsarin Mulkin Gabon, Dieudonne Aba’a Owono, sun sanya hannu kan yarjejeniyar cewar ƙasashen za su mutunta hukuncin kotun.
Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Mahmoud Ali Youssouf, wanda shi ma ya sanya hannu kan yarjejeniyar, ya yaba da warware takaddamar iyaka wadda ya ce ta ɗauki lokaci mai tsawo
Rikicin ya samo asali ne tun shekarar 1900, lokacin da ƙasashen mulkin mallaka na Faransa da Spain suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya a birnin Paris domin fayyace iyakokin yankunan da ke ƙarƙashin ikon su.
Ana kyautata tsammanin yiwuwar samun danyen mai a tsibiran na Cocotiers da Conga, lamarin da ya jefa kasashen biyu cikin gwagwarmayar ayyana mallakin sa shekaru 56 da suka gabata.