Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), reshen Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT), ta fara baje kolin bayanan sirri da takardun ’yan takarar da jam’iyyun siyasa suka gabatar domin shiga babban zaɓen shekarar 2027.
Hukumar ta bayyana cewa matakin ya dace da tanadin sashe na 29(3) na Dokar Zaɓe ta 2026, wadda ta wajabta mata nuna bayanan ’yan takara da takardun rantsuwa da sauran muhimman bayanai domin jama’a su samu damar bincika su.
An gudanar da aikin ne a babban ofishin INEC da ke Abuja, tare da gudanar da shi a lokaci guda a ofisoshin hukumar dake ƙananan hukumomin yankin (Area Councils) guda shida.
- Rukunin farko na dakarun wanzar da zaman lafiya sun isa Guinea-Bissau – NAF
- Jigawa – Gwamnati ta ware naira biliyan 13 domin magance zaizayar Ƙasa
- Ribadu ya bukaci sabbin masu gadin dazuka su kare al’ummomi cikin gaskiya da riƙon amana
Da take wakiltar Kwamishinan Zaɓe na FCT, Sakatariyar Gudanarwa ta hukumar, Hajiya Bimbo Oladunjoye, ta ce baje kolin bayanan ’yan takara wani muhimmin ɓangare ne na tsarin zaɓe domin tabbatar da gaskiya da buɗaɗɗen tsari.
Ta bayyana cewa bayanan da aka nuna sun haɗa da ’yan takarar shugaban ƙasa da kuma ’yan takarar Majalisar Tarayya da za su fafata a mazabun da ke cikin Babban Birnin Tarayya.
A cewarta, INEC na ci gaba da shirye-shiryen zaɓen 2027 tare da tabbatar da bin kundin tsarin mulki, Dokar Zaɓe ta 2026 da ƙa’idojin hukumar.
INEC ta sake tabbatar da aniyarta ta gudanar da zaɓe mai ’yanci, gaskiya, adalci da sahihanci, tare da kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su ba ta haɗin kai domin samun nasarar tsarin zaɓe.
Nuna bayanan ’yan takara kafin zaɓe na daga cikin matakan doka da aka tanada domin ƙara gaskiya da riƙon amana a harkokin zaɓe a Najeriya.