Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta yi jigilar rukunin farko na dakarun Najeriya da za su shiga aikin wanzar da zaman lafiya na ECOWAS a ƙasar Guinea-Bissau (ESSMGB).

Rundunar ta ce rukunin ya ƙunshi jami’ai da sojoji 86, ciki har da jami’ai 12 da sojoji 74, waɗanda suka tashi daga Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja cikin jirgin NAF kirar C-130 zuwa ƙasar Guinea-Bissau.

Ta bayyana cewa za a tura sauran dakarun a wani jirgin da zai biyo baya
Kafin tafiyarsu, an yi musu bankwana a Sansanin Ayyukan Sojojin Kula da Zaman Lafiya na Rundunar Sojin Ƙasa da ke Abuja, inda aka buƙace su da su kasance masu ƙwarewa, ladabi da riƙon amana a yayin gudanar da aikinsu.

An kuma tunasar da su cewa su ne jakadun Rundunar Sojin Ƙasa da Sojojin Najeriya da kuma Tarayyar Najeriya, don haka su kiyaye kyakkyawan suna da martabar ƙasar a duk tsawon lokacin aikin.

Rundunar ta ce wannan aiki ya nuna irin haɗin gwiwar da ke tsakanin sassan Sojojin Najeriya, tare da nuna ƙarfin Rundunar Sojin Sama wajen jigilar dakaru da kayan aiki domin tallafa wa ayyukan tsaro na cikin gida da na ƙasa da ƙasa.

NAF ta ƙara da cewa tura dakarun ya sake tabbatar da jajircewar Najeriya wajen tallafa wa ayyukan ECOWAS na wanzar da zaman lafiya da tsaro a yankin Afirka ta Yamma, tare da ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa da kuma inganta martabar Najeriya a duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *