Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Lauya Ezenwo Nyesom Wike, ya ba da umarnin rushe dukkan matsugunan da ba na ka’ida ba da kuma wuraren da ke zama matattarar barazana ga tsaro a tsawon hanyar jirgin kasa ta Kukwaba, kusa da Karmajiji, a tsakiyar birnin Abuja.

Umarnin ya fito ne a ranar Juma’a, 31 ga Yuli, 2026, sakamakon wani taron gaggawa na tsaro da aka gudanar a gidan ministan da ke Life Camp.

Bayan taron, Ministan ya jagoranci shugabannin hukumomin tsaro daban-daban na FCT zuwa shafin domin gudanar da dubawa na gani da ido.

Yayin da yake jawabi ga shugabannin tsaro a wurin taron, Lauya Wike ya jaddada muhimmancin gudanar da aiki na gaskiya da kuma amfani da bayanan sirri wajen dakile matsaloli tun kafin su tabarbare, maimakon zama kawai ana yanke shawara a ofis.

“Muna ganin inda rashin tsaro yake kyankyasar kansa, kuma ba za mu zuba ido ya kai matakin da zai yi wuyar sarrafawa ba. Dole mu dakatar da shi yanzu. Abin da na gani wata babbar barazana ce ga birnin nan. Na kasa yarda cewa irin wannan abun na iya kasancewa a nan,” in ji Lauya Wike.

Ministan ya jaddada cewa wadannan matsugunai da ba na ka’ida ba suna zama maboya ta sirri ga bata-gari, wanda ke zama babbar barazana ga tsaron mazauna babban birnin tarayya.

Bayan kammala duba hanyar jirgin kasa ta Kukwaba, Lauya Wike ya sake jaddada cewa za a dauki tsauraran matakai ba tare da tausayi ko nuna bambanci ba domin kare tsaron tsakiyar birnin.

“Mutane suna aikata laifuka sai su gudu su shiga nan; ba za ka iya sanin ko waye ke ina ba. Ta yaya za ka iya gano su ko gane inda suke? Kuma fa wannan yana tsakiyar birni ne. Ba mai yiwuwa mu tsaya muna kallo wannan ya ci gaba ba. Babu maganar tausayi a ciki… Zai kasance abu mafi muni idan muka bar irin wannan abun ya dore.”

Domin maido da doka da tsaro a yankin, Ministan na FCT ya ba Kwamishinan ‘Yan Sandan FCT, Ahmed Sanusi, umarnin yin aiki tare da Ma’aikatar Kula da Ci gaban Birni (Department of Development Control) domin rushe matsugunin da ba na ka’ida ba, sannan a tabbatar an hana bata-gari sake komawa wannan hanyar jirgin kasan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *