Gwamnatin Jihar Jigawa ta ware Naira biliyan 13 wajen aiwatar da manyan ayyukan magance zaizayar ƙasa domin kare al’ummomin da ke cikin haɗarin lalacewar muhalli da kuma tasirinta ga rayuka, hanyoyin samun abinci da kuɗaɗen shiga, da muhimman ababen more rayuwa.

Wannan ya haɗa da aikin Naira biliyan 10 da ake aiwatarwa tare da shirin Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL) a ƙauyukan Danmasara da Kalgo da ke Ƙaramar Hukumar Dutse, da kuma aikin magance zaizayar ƙasa na garin Kila da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram, wanda ake gudanarwa kan kuɗin kusan Naira biliyan 3.

Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan yayin da yake duba yadda aikin magance zaizayar ƙasa na Kila ke gudana. A yayin ziyarar, ya umarci kamfanin da ke aikin da ya faɗaɗa aikin domin samar da mafita mai ɗorewa ga matsalar muhallin.

Aikin Kila, wanda aka fara bayar da kwangilarsa kan kusan Naira biliyan 2.6, yanzu ya kai kusan Naira biliyan 3 bayan umarnin gwamnan na ƙara wasu ayyukan ƙarfafawa, ciki har da tsawaita shimfiɗar duwatsu (stone pitching) da kuma ƙarfafa hanyoyin magudanan ruwa

Gwamna Namadi ya ce an faɗaɗa aikin ne domin tabbatar da cewa zai daɗe yana aiki tare da samar da kariya mai ƙarfi ga mazauna yankin da suka shafe fiye da shekaru goma suna fama da barazanar zaizayar ƙasa

Yayin da yake duba aikin, gwamnan ya nuna gamsuwarsa da yadda aikin ke tafiya, amma ya umarci kamfanin da ya ƙara ƙarfafa wasu sassa domin tabbatar da cewa aikin zai jure tsawon lokaci.

Masana muhalli sun yi gargaɗin cewa sauyin yanayi da sauye-sauyen yanayin ruwan sama da kuma rashin ingantattun hanyoyin magudanan ruwa na ƙara haɗarin zaizayar ƙasa a sassa da dama na Najeriya.

Saboda haka, sun jaddada cewa saka hannun jari a ababen more rayuwa masu jure sauyin yanayi yana da matuƙar muhimmanci.

Ga mazauna garin Kila, faɗaɗa wannan aikin ya kawo sabon fata cewa matsalolin da suka shafe shekaru suna fama da su sakamakon zaizayar ƙasa da rashin tabbas za su zama tarihi nan ba da jimawa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *