Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta tura Kwamishinan ‘Yan Sanda Samuel Erale Etaifo zuwa jihar Osun domin jagorantar tsare-tsaren tsaro gabanin zaɓen gwamnan jihar da ke tafe.
A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce naɗin wani Kwamishinan ‘Yan Sanda na zaɓe (CP Elections) na daga cikin matakan tabbatar da zaman lafiya da tsaro da gudanar da sahihin zaɓe a jihar.
- Gwamnati ta fara raba gas na girki kyauta ga gidaje a Bayelsa
- ABU da NAHCON sun sanya hannu kan fara digiri a fannin gudanar da aikin Hajji
- COAS ya jaddada aniyar sojin Najeriya wajen bayar da agajin jin Ƙai
Sanarwar ta bayyana cewa CP Etaifo zai jagoranci daidaita ayyukan tsaro a lokacin zaɓen tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, domin kare masu kaɗa ƙuri’a da jami’an zaɓe da kayan aikin zaɓe.
Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Osun, CP Ibrahim Gotan, zai ci gaba da kula da harkokin yau da kullum na rundunar a jihar, tare da bai wa CP na zaɓe dukkan goyon bayan gudanarwa da ayyukan tsaro.