Ministan Ma’adinai na Najeriya, Dele Alake, ya umarci Hukumar Binciken Yanayin Ƙasa ta Najeriya (NGSA) da ta riƙa aika masa da rahoto kowane awa kan duk wani ci gaba da ya shafi girgizar ƙasa a kewayen Abuja, Babban Birnin Tarayya (FCT), domin ɗaukar matakan da suka dace, ciki har da sanar da sauran hukumomin da abin ya shafa idan ya zama dole
Ministan ya bayyana hakan ne a martani ga sanarwar da NGSA ta fitar, wadda ta ce an samu girgizar ƙasa da ta jijjiga wasu gine-gine a Abuja a ranar Talata, 4 ga Agusta
Yayin da yake kira ga mazauna Abuja da su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da fargaba ba, Alake, ya ce gwamnati ta riga ta ɗauki wasu matakan kariya domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a
- Dan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Accord ya janye domin mara wa Tinubu
- ‘Yan Sandan FCT sun kwato bindigogi da alburusai a Dajin Madam
- Shugaba Tinubu ya karawa sojoji albashi da kashi 80%
Cibiyar Sa-ido kan Girgizar Ƙasa NGSA da ke Utako ta bayyana cewa an auna girgizar da misalin karfe 11:23 da minti 27 na safe, inda ta samo asali daga zurfin kilomita ɗaya a ƙarƙashin ƙasa, sannan ta bazu har zuwa nisan kilomita huɗu cikin daƙiƙa biyar
Sai dai hukumar ta bayyana cewa girgizar ta kasar bata da wani tsanani da zata iya haifar da wata illa, tana tsakanin mataki na ɗaya zuwa na biyu (I–II) a ma’aunin Mercalli, wanda ake amfani da ita wajen auna tasirin girgizar ƙasa
Ministan ya tabbatar wa jama’a cewa NGSA za ta ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki, tare da jaddada cewa babu wani abin da zai hana mazauna Abuja ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.